Ba Mu Yi Takamaiman Shiri Don Fuskantar Real Madrid Ba — Guardiola
[ad_1]
Kocin Manchester City, Pep Guardiola, ya bayyana cewa har yanzu babu wani takamaiman shiri da ƙungiyarsa ta yi dangane da wasan da za ta buga da Real Madrid a gasar UEFA Champions League.
Manchester City za ta karɓi baƙuncin Real Madrid a filin wasan Etihad da ke birnin Manchester domin buga wasan zagaye na biyu na zagaye na 16 na gasar Zakarun Turai ta bana.
- Shugabar ALGON Ta Kano Ta Buƙaci Dakatar Da Aiyukan Siyasar Ado Doguwa
- Real Madrid Ta Shiga Halin Damuwa Bayan Wasanni Uku Ba Tare Da Nasara Ba
A wasan farko da aka buga a filin Santiago Bernabéu, Manchester City ta sha kashi da ci 3–0 a hannun Real Madrid. Duk da haka, Guardiola ya ce ƙungiyarsa za ta yi iya ƙoƙarinta domin ta rama a gidanta.
Guardiola ya shaida wa manema labarai cewa, “Har yanzu ban da wani takamaiman shiri kan yadda za mu tunkari wasan da Real Madrid.”
Tsohon kocin Bayern Munich ya ƙara da cewa ’yan wasansa sun san abin da ya kamata su yi domin kare martabar gida, yana mai cewa City na buƙatar cin kwallaye huɗu ba tare da an zura mata ko ɗaya ba domin ta kai zagayen kwata-fainal na gasar.
[ad_2]
Source link