An Fitar Da Takardar Bayani Kan “Kokarin Hongkong Na Kare Tsaron Kasa Karkashin Manufar ‘Kasa Daya Mai Tsarin Mulki Biyu’”
[ad_1]
Ofishin yada labarai na majalisar gudanarwa ta Sin ya fitar da takardar bayani kan “”Kokarin Hongkong na kare tsaron kasa karkashin manufar ‘kasa daya mai tsarin mulki biyu’” a yau 10 ga wata.
Ban da gabatarwa da kalmomin karshe, an tsara wannan takarda zuwa sassa biyar. Takardar ta nuna cewa, aikace-aikacen yankin Hongkong na kare tsaron kasar, a zahiri aiki ne da ake yi na nacewa ga raya manufar “kasa daya mai tsarin mulki biyu”, aikin dake kare ‘yanci da mutunci da walwalar mazaunan Hong Kong da yawansu ya kai miliyan 7.5, kuma aiki ne na inganta zaman lafiya da ci gaban duniya baki daya.
A duniya ta yau, ana kara fuskantar canje-canjen da ba a taba ganinsu a cikin karni guda ba, yanayin ci gaban kasar Sin na fuskantar sauye-sauye masu zurfi da sarkakiya, dole ne a ci gaba da aikin kare tsaron kasa ba tare da tsayawa ba. Gwamnatin kasar Sin tana ba da goyon baya mai karfi ga yankin musamman na Hong Kong don aiwatar da manufar “kasa daya mai tsarin mulki biyu” yadda ya kamata, ta yadda zai sauke nauyin dake wuyansa na kare tsaron kasa bisa tsarin mulkin kasa, ta kuma dada inganta tsaron kasa, don tabbatar da aikace-aikacen da za a gudanar karkashin manufar sun ci gaba da gudana ba tare da tangarda ba.
Yau Talata, kantoman yankin musamman na Hong Kong John Lee ya bayyana cewa, takardar bayani kan kokarin yankin Hong Kong na kare tsaron kasa bisa manufar “kasa daya, mai tsarin mulki biyu” tana da muhimmanci, kuma an gabatar da takardar a daidai lokacin da ya kamata, gwamnatin yankin musamman na Hong Kong za ta nuna cikakken goyon baya ga wannan takarda bisa dukkan fannoni, tare da aiwatar da abubuwan da takardar ta kunsa yadda ya kamata.
Ya ce, a matsayin kantoman yankin musamman na Hong Kong, zai jagoranci hukumomin kafa doka da kuma hukumar shari’a, ta yadda za su sauke alhakin da ke wuyansu na kare tsaron kasa. (Amina Xu, Maryam Yang)
[ad_2]
Source link