AFCON: Gabon Ta Soke Hukumar Ƙwallon Ƙafa Ta Ƙasar, Ta Dakatar Da Aubameyang
Daga Rabilu Sanusi Bena
Ministan wasannin kasar Gabon ya sanar da dakatar da tsoffin yan wasan tawagar kwallon kafar kasar Pierre-Emerick Aubameyang da Bruno Ecuele Manga, hakazalika ta dakatar da dukkan wadanda ke da alaka da babbar tawagar kasar, da kuma korar masu horar da tawagar bayan abinda ya kira rashin katabus da kasar tayi a Gasar Cin Kofin Afirka.
Kwallon da Bazoumana Toure ya jefawa Gabon a mintunan karshe na wasan da suka buga da Ivory Coast yayi sanadiyar ficewar Gabon daga gasar, Gabon ta sha kashi da ci 3-2 a hannun masu rike da kofin a wasan da suka buga ranar Laraba, rashin nasara sau uku a jere ya tabbatar da cewa Gabon sun kare a kasan rukunin F, wanda ya kunshi kasashenyan Ivory Coast, Kamaru da Mozambique.
Ganin yadda Panthers suka kasa tabuka abin Azo agani a gasar AFCON, gwamnati ta yanke shawarar korar duka masu horar da tawagar kasar, tareda dakatar da tawagar kasar har sai an samu sanarwa ta gaba, sannan ta kori yan wasa biyu da suka hada da Bruno Ecuele Manga da Pierre-Emerick Aubameyang,” in ji Minista Simplice-Desire Mamboula yayin hirar da yayi a Gidan talabijin na Gabon a daren Laraba.