Ƙungiyar ‘Dikko Na Kowa Ne’ Ta Jinjina Wa Gwamnan Katsina Bisa Biyan Ƴan Fansho Haƙƙoƙinsu

[ad_1]

Shugaban Ƙungiyar Dikko Na Kowa Ne, kuma sakataren ƙaramar Hukumar Funtuwa, Alhaji Hassan Musa Anda Funtuwa ya jinji wa Gwamnan Jihar Katsina, Dakta Umar Dikko Raɗɗa bisa biyan ma’aikatan da suka yi ritaya haƙƙoƙinsu na sama da naira biliyan 21 ga ma’aikatan jihar da na ƙananan hukumomi da na malamam makarantar firamare.

Alhaji Hassan ya tabbatar da cewa biyan waɗannan kuɗaɗe zai farfaɗo da tattalin arzikin Jihar Katsina kuma zai taimakawa gaya wajen ci gaban jihar.

  • Gwamnatin Tarayya Ta Buɗe Makarantar Koyar Da Harsuna A Kano
  • Kasar Sin Ta Bayar Da Gudunmuwar Kayayyakin Bukata Ga Matan Sudan Ta Kudu

A cewarsa, Gwamna Raɗɗa ya aje tarihi a Jihar Katsina da ma ƙasa baki ɗaya na biyan waɗannan biliyoyin nairori a lokaci guda. Ya ce lallai wannan ya tabbatar wa ma’aikatan Jihar Katsina cewa Dikko nasu ne mai jinƙansu ne, duk wanda ritayarsa ya yi kusa ba zai yi fargabar aje aikinsa ba.

Da ya koma kan batun ayyukan ƙungiyarsu ta Dikko Na Kowa Ne, Hassan ya bayyana cewa a biyan ma’aikatan da suka aje aikinsu a jihar, ya tabbatar musu da cewa wannan sunan na Dikko Na Kowa Ne ya tabbata a garesu, saboda Gwamna Dikko ya ba da fifiko a kowane vangare na ci gaban al’ummar Jihar Katsina baki ɗaya.

Haka kuma ya ce wannan ƙungiyar za ta shiga lunguna da sako wajen tallata ayyukan da Gwamna Dikko ya yi wa al’umma domin su ci gaba da yi masa addu’a na ganin burinsa ya cika na ci gaban Jihar Katsina baki ɗaya.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *