ISWAP ta sace ’yan mata 13 a Borno

[ad_1]



Mayaƙan ISWAP sun sace wasu ’yan mata a Ƙaramar Hukumar Askira-Uba a Jihar Borno.

Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Borno, Abdullahi Askira, ya tabbatar da sace ’yan matan.

Ya ce an sace ’yan natan ne yayin da suke aiki a gonakinsu da ke yankin Mussa.

A cewarsa, ’yan matan guda 13 masu shekaru tsakanin 15 zuwa 20 sun tafi gona domin girbe amfanin gonarsu, sai maharan suka yi awon gaba da su.

Tun da farko an mayar da mutanen Huyim zuwa Mussa saboda matsalar rashin tsaro a garuruwansu.

Sai dai ya ce ɗaya daga cikin ’yan matan da aka sace ta tsere kuma ta koma gida a safiyar ranar Lahadi, amma sauran 12 har yanzu suna hannun maharan.

Sanata Mohammed Ali Ndume, wanda ke wakiltar yankin, ya yi kira ga hukumomin tsaro da su ceto ’yan matan cikin ƙoshin lafiya.

Ya kuma roƙi al’ummar yankin da su ci gaba da yin addu’a, tare da sanar da hukumomi duk wani abun zargi.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *