Ɗalibai 50 Da Aka Sace A Neja Sun Tsere CAN

[ad_1]


Ƙungiyar Kiristoci ta Nijeriya (CAN) reshen Jihar Neja ta tabbatar da cewa ɗalibai 50 daga cikin waɗanda aka sace daga Makarantar Sakandare da Firamare ta St. Mary’s, Papiri, a ƙaramar hukumar Agwara, sun tsere daga hannun waɗanda suka yi garkuwa da su. Hare-haren dai sun faru ne da safiyar Juma’a, inda maharan suka kashe ɗan banga sannan suka yi awon gaba da sama da mutane 200, ciki har da malamai 13.

A rahotonsa na farko, Shugaban CAN na Jihar Neja, Most Rev. Bulus Dauwa Yohanna, wanda shi ne mai makarantar, ya ce an sace ɗalibai 215 tare da malamai 12. Sai dai daga baya, a ranar Asabar, ya bayyana cewa an gano cewa wasu ƙarin dalibai 88  sun ɓace bayan sake yin ƙididdiga. A sanarwar da mai taimaka masa, Daniel Atori, ya fitar a madadinsa a ranar Lahadi, ya tabbatar da cewa ɗalibai 50 sun samu damar tserewa kuma sun haɗu da iyayensu.

Rev. Yohanna ya bayyana cewa makarantar na da tsarin kwana da na zuwa gida, inda 377 daga cikin ɗalibai 430 na firamare ke zaune a makarantar, yayin da 53 ke zuwa daga gida. Ya ce a halin yanzu, baya ga waɗanda suka tsere, ɗalibai 141 ba su shiga cikin waɗanda aka sace ba, yayin da ɗalibai 236, yara guda uku ƴaƴan ma’aikata, da ɗaliban sakandare 14 da ma’aikata 12 ke hannun masu garkuwa.

Hukumomin tsaro dai sun ce suna ƙara ƙaimi wajen ganin sun ceto sauran mutanen da ke hannun maharan.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *