Yadda jami’an tsaro suka kashe ’yan ta’adda a musayar wuta 50 a Neja

[ad_1]



Jami’an tsaro sun halaka aƙalla ’yan ta’adda 50 a yayin wata musayar wuta a yankin Ƙaramar Hukumar Mariga da ke Jihar Neja.

Hadin gwiwar sojoji da sauran tsaro sun aika ’yan ta’addan lahira ne a yayin wani ƙazamar arangama a yankin Kumbashi da ke Ƙaramar Hukumar.

Shugaban Majalisar Dokoki ta Jihar Neja, muka wakilin Ƙaramar Hukumar Mariga a majalisar, Abdulmalik Sarkin-Daji, ya bayyana cewa jami’an tsaron sun yi nasarar kuɓutar da wasu mutane da ’yan ta’addan suka yi garkuwa da su.

Abdulmalik Sarkin-Daji, ya sanar da haka ne a Kontagora, yana mai jinjina wa jami’an tsaro.

Ya ruwaito shaidu na cewa ’yan ta’adda kimanin 300 ɗauke da makamai ne suka yi yunƙurin kutsawa ƙauyen  a ranar Talata.

“Sun yi nufin kai hari ne a wani sansanin Hukumar Tsaro ta DSS, amma jami’an tsaron suka mayar da martani suka kashe kimanin 50 daga cikin ’yan bindigar wasu da dama suka tsere ɗauke da raunukan harbi.

“Al’ummar mazaɓata sun tabbatar min cewa sun ga yadda ’yan ta’addar saboda tsabar girgiza, suka riƙa sassara gawarwakin abokansu suna sanyawa a cikin buhuna, suna tafiya da su a kan baburansu.”

A wani labari makamancin wannan kuma, ’yan bindiga sun kashe wani manomi tare da jikkata wasu a yankin Kundu da ke kusa da garin Zungeru a Ƙaramar Hukumar Rafi a ranar Alhamis.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *