ASUU da Gwamnatin Tarayya sun sake tattauna yarjejeniyar 2009
[ad_1]
Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU) da Gwamnatin Tarayya, sun kammala tattaunawa kan sabunta yarjejeniyar shekarar 2009.
Sabuwar yarjejeniyar za ta fara aiki daga ranar 1 ga watan Janairun 2026, kuma za a sake duba ta duk bayan shekaru uku.
Yarjejeniyar ta ƙunshi inganta rayuwar malaman jami’o’i da kuma ƙara wa jami’o’i kuɗaɗen tallafi.
Ma’aikatan jami’o’i za su samu ƙarin albashi da kashi 40 cikin 100, yayin da Farfesoshi da za su yi ritaya a shekara 70 za su samu fansho daidai da albashinsu na shekara.
Haka kuma, jami’o’in gwamnati za su samu ƙarin kuɗi don gudanar da bincike, ɗakunan karatu, ɗakunan gwaje-gwaje, kayan aiki, da horar da ma’aikata.
Za a kafa Hukumar Bincike ta Ƙasa domin tallafa wa bincike, inda kuɗin da za a ware ya kai aƙalla kashi ɗaya cikin 100 na kuɗaɗen shigar Najeriya.
Yarjejeniyar ta ƙara samar da ’yancin gudanar da jami’o’i da ’yancin ilimi, ta bai wa Farfesoshi damar zaɓar shugabanni kamar deans da provosts, sannan ta tabbatar da cewa ba za a hukunta malamai da suka yi yajin aiki a baya ba.
ASUU ta buƙaci gwamnati ta aiwatar da yarjejeniyar cikin gaggawa tare da faɗaɗa tattaunawar da sauran ƙungiyoyin jami’o’i domin tabbatar da tsarin ilimi.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link