Zulum ya bai wa hukumomin tsaro kyautar motoci 63 don inganta tsaro a Borno
Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya raba wa hukumomin tsaro da rundunar haɗin gwiwa ta CJTF kyautar motoci 63 don inganta tsaro a Maiduguri.
Daga cikin motocin, an bai wa rundunar CJTF guda 30, jami’an tsaro 16, ƙungiyoyin tsaro 10, mafarauta shida, sannan aka bai wa hukumar NAPTIP guda ɗaya.
An raba motocin ne domin inganta sintiri da kai ɗaukin gaggawa, domin yaƙi da laifuka da barazanar tsaro irin su ’yan daba da sauran masu aikata laifi a Maiduguri da kewaye.
Wannan na cikin irin tallafin da Gwamna Zulum ke bayarwa don inganta tsaro da kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
Yayin ƙaddamar da rabon, Gwamna Zulum ya jaddada ƙudirin gwamnatinsa na ci gaba da tallafa wa jami’an tsaro da kayan aiki domin gudanar da aikinsu yadda ya kamata.
Ya ce: “Gwamnatinmu za ta ci gaba da bai wa jami’an tsaro dukkanin goyon bayan da ake buƙata don tabbatar da zaman lafiya da tsaro a Jihar Borno.”
Zulum ya kuma gode wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, da dukkanin jami’an tsaro bisa ƙoƙarinsu na wanzar zaman lafiya a jihar.
Taron rabon ya samu halartar Mataimakin Gwamnan Jihar Borno, Dakta Umar Usman Kadafur, Sakataren Gwamnati Bukar Tijani.
Sauran sun haɗa da Kwamishinan ’Yan Sanda, Naziru Abdulmajid, Daraktan Hukumar Tsaro, Adamu Umar da sauransu.