Yadda Fatar Ki Za Ta Yi Laushi Da Sheki
[ad_1]
Gyaran fata abune mai matukar kyau ga mace, idan kina so ki ganki kullum cikin kyau tofa sai kin cire kiwa kina kokarin gyaran fata. Za kiga fatanki tana sheki, ta yi laushi, ruwa ko zama baya yi akai.
Abubuwan bukata:
Man zaitun, Lalle, Kurkur, Madara peak.
Yadda ake hadawa:
Za ki hade wadannan kayan hadin da na ambata a guri daya, sai ki kwaba su ki shafe jikinki da fuskarki, za kiyi wannan hadin kafin ki shiga wanka. Idan ya bushe a jikinki sai ki murje sannan sai ki shiga wanka jiki yana yin kyau yayi sheki.
Gyaran jiki 2
Wannan hadin shi akecewa kafi Turgewa.
Abubuwan da ake bukata:
Kur-kur, Dulka, Zuma, Kwai, Lemun tsami.
Yadda ake hadawa:
Ki hade su guri daya ki kwaba kamar yadda ake kwaba lalle, amma yafi kwabin lalle ruwa, sai ki shafe fuskarki.
Idan kuma har dajiki kike so, sai ki shafa harda jiki bayan awa daya sai ki shiga wanka za ki ga yadda jikinki zai goge.
Gyaran jiki 3
Fata ta yi laushi da sheki
Abubuwan da ake bukata:
Lalle, Kwaiduwar kwai guda 3, Manja cokali 3, Kur-kur:
Yadda ake hadawa:
Sai ki kwaba su guri daya ki shafe jikinki zuwa awa daya, sai kiyi wanka da ruwan dumi, Sannan ki kara shafe jikinki da ita sai ki kuma yin wanka.
Kyan fuska 1:
Abubuwan da ake bukata:
Dettol, Sabulun Ghana, Garin zogale, Farar albasa.
Yadda ake hadawa:
Sai ki hade su guri daya ki kirba su cikin Turmi, ki mulmula ki rinka wanke fuska za ki ga yadda fuskar ki za tayi.
Gyaran fuska 2
Wanna hadin wanda ya kesa fuska tayi haske da annuri ta kuma kore kurajen fuska.
Abubuwan da ake bukata:
Bawon kankana.
Yadda ake hadawa:
A samu bawon kankana sai a rinka goge fuska da shi yana gyara fuska tayi sumul.
Gyaran Fata 1
Abubuwan da ake bukata:
Lemun tsami, bawon kwai, Kur-kur.
Yadda ake hadawa:
Za ki hade su guri daya sai ki daka su, ki rinka wanka dashi fatar mace za ta goge tayi kyawun gaske.
Gyaran fata 1
Abubuwan da ake bukata:
Ganye magarya, Sabulun salo.
Yadda ake hadawa:
Za ki daka Ganyan magarya sai ki zuba a cikin sabulun salo ki rinka wanka yana gyara jiki.
Gyaran fata 2
Abubuwan da ake bukata:
ganyan magarya, Man zaitun, Man habbatussauda.
Yadda ake hadawa:
Ana daka ganyan magarya a zuba cikin Man zaitun da Man habbatussauda shi ma yana gyara.
Gyaran fata 3
Abubuwan da ake bukata:
Lalle, Garin ridi.
Yadda ake hadawa:
Ana amfani da Lalle kafin ki shiga wanka sai ki kwaba ki zuba garin ridi ki shafe jikinki zuwa awa daya sai kiyi wanka.
Maganin tabo a jiki:
Ki samu khal babban cokali daya sai ki hada da ruwa Kofi biyu ki tafasa bayan ya huce sai ki rinka shafawa a jiki da fuskar.
Maganin Nankarwa
alama) A turance
Nankarwa shine irin wannan zanen da yake fitowa a cikin mace da zaran ta fara haihuwa ko kuma in tayi kiba a ciki, mace ya kan fitowa ya sanya fatar cikin duk ta yamutse ana amfani da Man Dodon kodi a shafa a ciki, yana gyara fatar ciki ta koma kamar ba ta haihu ba.
Maganin nankarwa 2
Abubuwan bukata:
Man kadanya, Man zaitun, Lemun tsami.
Yadda ake hadawa:
Ki hada Man kadanya da Man zaitun guri daya, ki matsa lemun tsami a kai, amma ba da yawa ba, ki matsa sosai sannan sai ki dinga sharewa ki yawaita yi.
Maganin nankarwa 3
Ana shafa zuma farar saka da daddare, idan za ki kwanta barci da safe sai ki samu ruwan dimi ki wanke.
[ad_2]
Source link