Yunwa na kashe ’yan Najeriya, amma Tinubu ko a jikinsa – Atiku
[ad_1]
Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya yaba wa ’yan Najeriya bisa abin da ya kira ‘hakurinsu, juriya da kwazo’ duk da tsananin matsin tattalin arziki da rashin tsaro da suke fama da shi.
A cikin sakonsa na murnar cikar Najeriya shekaru 65 da samun ’yancin kai da ya aike ga ’yan kasa, Atiku ya zargi gwamnatin jam’iyyar APC da watsi da al’umma, yana mai cewa sun bar ’yan Najeriya su fama da rayuwa mai cike da kalubale ba tare da kulawa ba.
Atiku ya ce “’yan Najeriya na fama da tsananin rashin tsaro, karancin abinci, rashin aikin yi da kuma yanayi mai cike da fargaba da rashin kyakkyawar makoma wanda ya kara muni sakamakon rashin tausayi da rashin kulawar gwamnatin APC.
“Abin takaici ne cewa a cikin kasa mai albarka da arziki, miliyoyin mutane sun koma ’yan gudun hijira da mabarata a cikin kasarsu. Kowace gwamnati mai kishin kasa tana daukar rayuwa da tsaron ’yan kasa da muhimmanci.
“Amma abin da muke fama da shi a yau shi ne gwamnatin da ta watsar da jama’arta. Yunwa na kashe ’yan Najeriya, ’yan bindiga na hallaka al’umma, amma Shugaba Bola Tinubu da ministocinsa suna kallon abubuwa suna faruwa ba tare da nuna damuwa ba.”
Sai dai Atiku ya bukaci ’yan kasa da kada su yanke kauna, yana mai tunatar da su cewa shekarar 2027 na tafe da damar sauya shugabanci mara nagarta da kuma dawo da rayuwa mai kyau.
“Kyawun dimokuradiyya yana cikin ikon kada kuri’a. Ko da kuwa jama’a na cikin kunci da zalunci a yau, za su samu damar kawar da wannan gwamnati mara iya aiki a zabe mai zuwa. Wannan iko ne da babu wata kungiya da za ta iya kwacewa daga hannun jama’a,” in ji shi.
A cewarsa, duk da cewa Najeriya ta cika shekara 65 da samun ’yancin kai, har yanzu tana tafiyar hawainiya sakamakon shekaru da dama na shugabanci mara nagarta da almubazzaranci.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link