Yoweri Museveni Ya Yaba Da Ingantuwar Dangantaka Tsakanin Sin Da Uganda

[ad_1]

Shugaban Uganda Yoweri Museveni, ya ce dangantakar da ke tsakanin kasarsa da Sin ta ci gaba da karfafa a shekarun baya bayan nan, kuma manufar Sin ta soke haraji baki daya, kan kasashen Afrika zai taimaka wajen bunkasa fitar da kayayyaki daga Uganda zuwa kasar ta 2 mafi karfin tattalin arziki a duniya.

Cikin wata sanarwa da fadar shugaban ta fitar jiya, shugaba Museveni ya yaba da yadda dangantakar kasashen biyu ke ci gaba da karfafa.

Shugaban wanda ya yi nasarar ci gaba da mulkin kasar a wa’adi na 7, ya bayyana bayan lashe zaben shugaban kasar a makon jiya cewa, yana maraba da matakin gwamnatin Sin na soke haraji kan kayayyakin da Uganda ke shigarwa kasar, yana cewa wannan mataki ya taimaka gaya wajen bunkasa harkokin cinikayya na Uganda da kuma kokarinta na samun kudin shiga.

Da ya tabo batun jarin Sin a Uganda, shugaban ya ce sun dade suna goyon bayan muradun kasar Sin, kuma za su ci gaba da yin hakan.

Yoweri Museveni ya bayyana haka ne lokacin da ya ke ban kwana da jakadan Sin a kasar mai barin gado Zhang Lizhong, wanda ya godewa shugaban da gawamnatin Uganda bisa goyon baya da hadin gwiwar da suka ba shi a wa’adinsa na aiki. (FMM)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *