A gaggauta binciko makasan ’yar jaridar Arise TV —Tinubu

[ad_1]



Shugaba Bola Ahmed Tinubu tare da uwargidansa, Sanata Oluremi Tinubu sun bayyana alhini kan kisan gillar da aka yi wa  Somtochukwu ‘Sommie’ Maduagwu, waata ’yar jarida mai gabatar da labarai a gidan Talabijin na ARISE TV.

A wata sanarwa da fadar shugaban ƙasa ta fitar, shugaba Tinubu da uwargidansa sun yi Allah-wadai da kisan, suna mai bayyana cewa a matsayin babban rashi a ƙasar da kuma fagen aikin jarida.

Aminiya ta ruwaito cewa, marigayiyar ta rasu ne bayan wani farmaki da ’yan fashi suka kai gidanta da ke Katampe a Abuja, a ranar Litinin da ta gabata.

Tinubu ya yi kira ga hukumomin tsaro da su gaggauta gudanar da cikakken bincike, tare da tabbatar da cewa wadanda suka aikata laifin sun fuskanci hukunci kamar yadda doka ta tanada.

Ita ma uwargidan shugaban ƙasar ta bayyana marigayiyar a matsayin jaruma mai ƙwarewa da gaskiya a aikinta, tana mai cewa murya irin tata tana da tasiri matuƙa wajen wayar da kai da isar da gaskiya ga al’umma.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *