Ronaldo Zai Iya Buga Wasan Farko Na Kofin Duniya Bayan Hukuncin FIFA

[ad_1]


Kyaftin ɗin ƙasar Portugal, Cristiano Ronaldo, zai iya buga wasan farko na gasar cin Kofin Duniya mai zuwa, bayan da FIFA ta soke hukuncin dakatar da shi daga wasanni biyu.

An kori Ronaldo ne a wasan neman gurbin Kofin Duniya da Portugal ta yi da Ireland, sakamakon dukan da ya yi wa O’Shea da gwiwar hannu.

Wannan ya sa bai buga wasan ƙarshe da Portugal ta yi da Armenia ba, wanda suka ci 9-1 suka kuma samu tikitin zuwa Kofin Duniya.

FIFA ta ce an dakatar da Ronaldo na wasanni uku, amma idan bai sake aikata irin wannan ba, ba za a hukunta shi ba.

Sai dai ta ƙara da cewa idan ya sake yin kuskure makamancin haka cikin shekara guda, za a dawo da dakatarwar wasanni biyun, a kuma aiwatar da ita a kowace gasa da FIFA ta amince da ita.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *