An ƙara rage kuɗin aikin Hajjin 2026 a Najeriya




An ƙara rage kuɗin kujerar aikin hajjin bana zuwa aƙalla Naira miliyan 7.5 ga maniyyata daga jihohin Arewacin Nijeriya.

Shugaban Hukumar, Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan ne ya bayyana haka a wata tattaunawa da manema labarai.

Ya ce an rage kuɗin ne sakamakon umarnin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu na yin hakan da kuma tattaunawar da suka yi ta baya-bayan nan da kamfanonin Saudiyya.

A ƙarƙashin sabon farashin yanzu jihohin da ke shiyyar Borno/Adamawa za su biya Naira 7,579,0202 maimakon Naira 8,327,125 da hukumar ta sanar a baya.

Sauran jihohin Arewa kuma sabon farashinsu shi ne Naira 7,669,769 maimakon Naira 8,457,685 da aka sanar da farko.

Jihohin Kudancin Nijeriya kuwa za su biya Naira 7,991,141 saɓanin Naira 8,784,085.

Sai dai yanzu an kayyade ranar 05 ga watan Disamba ta zama wa’adin ƙarshe da duk maniyyatan Nijeriya za su cika kuɗin kujerarsu.




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *