Bayanan Tattalin Arziki: Yadda Kasar Sin Ke Ci Gaba Da Zama Mai Ciyar Da Tattalin Arzikin Duniya Gaba
[ad_1]
Kwanan nan, wasu kafafen yada labarai da hukumomi na kasashen yamma sun sake yin kalamai irin su “tattalin arzikin Sin ya kai matsayin koli na raguwa nan gaba”, “injin ci gaban Sin ya tsaya”. Amma, jerin bayanai masu inganci a farkon shekarar 2026 suna mayar da martani ga wadannan maganganu. Tun daga farfadowar bukatun cikin gida zuwa kara bude kofa ga ketare, daga ci gaban GDP mara yankewa zuwa habakar masana’antar AI mai karfi, har yanzu tushen tattalin arzikin Sin yana da karfi, kuma ana samun karuwar karfin gaggauta samun ingantaccen ci gaba.
Saya da sayarwa su ne babban injin ciyar da tattalin arziki gaba. A watannin Janairu da Fabrairu na 2026, jimillar sayarwa da samar da hidimomi na al’ummar Sin ta kai kusan Yuan tiriliyan 8.61, wadda ta karu da kashi 2.8% idan aka kwatanta da ta shekarar da ta gabata, kuma adadin karuwarta ya fi na watan Disambar shekarar da ta gabata sauri da kashi 1.9%.
Sin ta ci gaba da rike manufar bude kasuwa ba tare da karkacewa ba. A watannin Janairu da Fabrairu na wannan shekara, cinikayyar shige da fice tsakanin Sin da ASEAN da EU ta karu da kashi 20.3% da 19.9% bi-da-bi, kuma cinikayyar shige da fice tsakanin Sin da kasashe da yankunan da shawarar ziri daya da hanya daya ta shafa ta karu da kashi 20%. Bugu da kari, kamfanonin kasashen waje suna nuna amincewa da kwarin gwiwarsu ga Sin bisa ainihin matakai da aka dauka. Hukumar yin kwaskwarima a gida da bude kofa ga waje ta kasar Sin ta fitar da shiri karo na 9 na shigar da jarin ketare wajen gudanar da manyan ayyuka guda 13, inda ake sa ran shigo da jarin ketare dala biliyan 13.4. Ya zuwa yanzu, an shigo da dala biliyan 108 a duk wadannan manyan ayyukan a kowane karo na shirin, kuma matakin ya ba da misali da jagoraci mai kyau ga aikin shigo da jarin ketare.
Fasahar AI tana zama sabon injin ciyar da tattalin arzikin Sin gaba. A taron manyan jami’ai na ci gaban kasar Sin da aka gudana kwanan nan, shugaban hukumar tara bayanai ta kasar Liu Liehong ya bayyana cewa, ana hasashen a karshen shirin ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al’ummar Sin na shekaru biyar-biyar karo na 15, girman masana’antar AI da abubuwa masu alaka a Sin zai kai adadin kudi fiye da Yuan tiriliyan 10. An yi wannan hasashe ne bisa hakikanin halin da ake ciki: a farkon shekara ta 2024, yawan “token” ta AI da aka yi amfani da su a Sin ya kai biliyan 100 a kowace rana, inda ya haura zuwa tiriliyan 100 a karshen shekara ta 2025, kuma a watan Maris na wannan shekara ya wuce tiriliyan 140, inda ya karu fiye da sau 1000 cikin shekaru biyu kacal. A matsayinta na kasa daya tilo a duniya da ke da cikakkun nau’ikan masana’antu, fa’idodin Sin na musamman a fannonin albarkatun bayanai, tsarin masana’antu da girman kasuwa, suna taka rawa wajen mayar da karfin fasaha zuwa karfin ci gaba cikin sauri.
Sin kullum tana samun bunkasar tattalin arzikinta ba tare da tangarda ba, duk da fuskantar wahalhalu da matsaloli da mawuyancin hali. Ko da yaushe ana karyata maganganun da wasu kasashen yamma suka saba yi da hakikanin gaskiya. Bayanan farkon shekara ta 2026 sun isar da sako a fili cewa, kasuwar cikin gidan Sin tana farfadowa a hankali, tsarin bude kofa ga ketare yana ci gaba da karuwa, kuma sabon karfin samar da kayayyaki da hidimomi masu karko yana habaka cikin sauri. Kamar yadda asusun ba da lamuni na kasa da kasa (IMF) ya fada a baya, Sin ta kasance muhimmiyar injin ciyar da tattalin arzikin duniya gaba. Abu mafi muhimmanci shi ne, Sin mai yanayin kwanciyar hankali, wadata da bude kofa, ta kasance mai ciyar da tattalin arzikin duniya baki daya gaba. Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya taba cewa: “Idan duniya ta yi kyau, to Sin za ta yi kyau, idan Sin ta samu ci gaba mai armashi, to duniya za ta ci gajiya” – ci gaban Sin mai inganci, ba kawai yana ba da kwarin gwiwa ga duniya ba, har ma yana kasancewa karfin gaggauta ci gaban duniya na zahiri.(Marubuci: MINA)
[ad_2]
Source link