Me Ya Sa Shugabannin Kasashen Turai Suka Yi Ta Ziyartar Kasar Sin?
[ad_1]
Tun daga ranar 28 zuwa 31 ga watan Janairun bana, firaministan kasar Birtaniya, Keir Starmer, ya kawo ziyarar aiki kasar Sin, inda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da shi a ranar 29 ga wata a Beijing. Bangarorin biyu sun cimma jerin yarjeniyoyi masu gamsarwa, al’amarin da ya bude sabon babin hulda da hadin-gwiwar kasashen biyu.
Tun daga karshen shekarar da ta gabata wato 2025, akwai shugabannin kasashen Turai da dama da suka kawo ziyara kasar Sin, ciki har da na Sifaniya, da Faransa, da Ireland, da Finland da kuma Birtaniya. To, shin mene ne dalilin hakan?
A bana ne ake kaddamar da aiwatar da shirin raya kasar Sin na shekaru biyar-biyar karo na 15, inda samar da ci gaba mai inganci, da fadada bude kofa ga kasashen waje bisa matsayin koli, ya kasance sako na zahiri da kasar Sin ta gabatar wa dunniya. A halin yanzu, ci gaban kasashen Turai da dama na tafiyar hawainiya, inda suka yi fatan amfani da damarmaki da kasar Sin ta bayar, don sanya babban kuzari ga tattalin arzikinsu. Kazalika, ra’ayin nuna bangaranci da na bada kariya da ra’ayin nuna fin karfin siyasa ya kara zama ruwan dare a duk fadin duniya, inda kasashen Turai suka kara fahimtar bukatar daidaita huldodi da manyan kasashe, a wani kokari na kyautata dangantakarsu da kasar Sin ta hanyar da ta dace.
A matsayinsu na muhimman kasashen da ke kiyaye tsarin duniya, hadin kan kasar Sin da kasashen Turai, fa’ida ce ga duniyarmu da ke fama da tashe-tashen hankula a halin yanzu. Shugaba Xi ya bayyana wa shugabannin kasashen Turai ra’ayinsa kan batun dakile hadarurruka gami da dimbin kalubalen duniya, yana mai cewa, ya dace manyan kasashe su jagoranci aikin shimfida adalci, da bin doka da oda, da karfafa hadin-gwiwa da aminci, kana, dokokin duniya ba za su taka rawar gani ba har sai kasa da kasa sun mutunta su.
A nasu bangaren kuma, shugabannin kasashen Turai da dama sun jinjina wa kasar Sin saboda muhimmiyar rawar da ta taka ga harkokin duniya, inda a cewarsu, za su goyi bayan ra’ayin kara cudanyar mabambantan sassa, da gudanar da kasuwanci cikin ’yanci, al’amarin da a ganin manazarta, ya shaida niyyar kasar Sin da kasashen Turai wurin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya cikin hadin-gwiwa. (Murtala Zhang)
[ad_2]
Source link