An Damke Wani Mutum Kan Mutuwar Abokinsa A Wurin Liyafar Cin Abnici A Edo

[ad_1]

Daga Rabiu Ali Indabawa

Rundunar ’Yansandan Jihar Edo ta tabbatar da kama wani mutum mai suna Eghosa Osas bisa zargin kashe abokinsa tun suna yara, Amadin Williams.

Jami’ar hulda da jama’a ta rundunar, Eno Ikoedem, ta tabbatar da kamun ga PUNCH Metro.

Rundunar ta kara da cewa za a gurfanar da wanda ake zargi a gaban kotu da zarar an kammala bincike.

A cewar wata majiya da ke kusa da lamarin, marigayin ya dawo daga kasashen waje tare da iyalinsa domin bikin Kirsimeti.

An ce an kai masa hari tare da kashe shi ne a unguwar Oben, inda ya je halartar bikin liyafar bude sabon gida.

Majiyar ta ce, “Zan iya tabbatar da cewa Eghosa Osas mai shekaru 43 an kashe shi ne da hannun abokinsa tun suna yara, Amadin Williams, dalilan da suka jawo hakan kuma har yanzu ba a tabbatar da su ba.

“Marigayi Eghosa ya dawo daga kasashen waje ne domin yin bikin Kirsimeti tare da iyalinsa.

“An ce an kai masa hari tare da kashe shi a unguwar Oben, inda ya halarci bikin bude sabon gida.”

Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Edo, Eno Ikoedem, wadda ta tabbatar da faruwar lamarin, ta ce babban dan’uwan marigayin ne ya kai rahoton kisan.

Ikoedem ta ce Eghosa ya fita ne domin yin bayan gida, sai wanda ake zargin ya tare shi ya sare shi da adda a wuya, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwarsa.

Ta kara da cewa wanda ake zargin ya tsere amma daga bisani aka kama shi a Birnin Benin, babban birnin Jihar Edo, inda ta jaddada cewa nan ba da jimawa ba za a gurfanar da shi a gaban kotu.

Ta ce, “Rahoton kisan Eghosa gaskiya ne, kuma wanda ake zargi, Amadin Williams, wanda ake kyautata zaton abokinsa ne tun suna yara, shi ne ake zargi da aikata laifin.”

“Bincike na ci gaba da gudana, kuma za a gurfanar da wanda ake zargi a gaban kotu da zarar an kammala shi (binciken),” in ji ta.

Wani makamancin lamari ya faru a watan Yuni, inda ’yansanda suka kama wani mutum mai shekaru 31, Joshua Osaigbobo, akan mutuwar budurwarsa, Osato Festus Edogiaweria mai shekaru 21, wadda aka ruwaito ta bace tun a watan Afrilun 2025.

’Yansanda sun ce sun fara bincike ne bayan mahaifiyar wacce aka kashe, Ojo, ta kai rahoton bacewar ’yarta a ofishin ’yan sanda na Aduwawa a ranar 25 ga Afrilun 2025.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *