[ad_1]
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ta kama mutum 26 da ake zargin masu garkuwa da mutane ne tare da kwato makamai da kudade daga hannunsu.
Daga cikin abubuwan da aka samu nasarar kwatowar har da bindigogi na gida guda huɗu, makamai masu hatsari da kuma tsabar kuɗi Naira 546,000 da ake zargin wani ɓangare ne na kuɗin fansa.
An kama waɗanda ake zargin ne a cikin jerin samame da aka gudanar daga ranar 3 zuwa 5 ga watan Oktoban 2025, a sassa daban-daban na jihar.
Samamen ya haɗa jami’ai daga sashen ’yan sanda na Anchau, Hukumar Kula da Tsaro ta Jihar Kaduna (KADVIS), da kuma sashen yaƙi da garkuwa da mutane na rundunar.
Bayanin samamen na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, DSP Mansir Hassan, ya fitar a ranar Alhamis.
Ya ce cikin wani samame da aka kai da safiyar ranar 5 ga watan Oktoba, an kama mutane shida, ciki har da wani Jibrin Abubakar wanda aka fi sani da “Oga,” bayan samun sahihan bayanan sirri.
Waɗanda ake zargin sun yi garkuwa da wani mutum mai shekaru 60 da haihuwa mai suna Idris Adamu, a ranar 22 ga Satumba, inda suka tsare shi na tsawon kwanaki kafin su sako shi bayan sun karɓi kuɗin fansa na naira miliyan biyar.
An kuma kama wasu mutane biyu bayan musayar wuta da ’yan sanda, yayin da wasu biyu suka cika wandonsu da iska.
A lokacin samamen, ’yan sanda sun kwato bindigogi biyu na gida kirar pump-action, harsasai biyar da ba su da ciko, laya, da kuma kuɗi naira 546,000 da ake zargin wani ɓangare ne na kuɗin fansa.
A wani samame daban da aka gudanar a ranar 3 ga Oktoba kuma, an kama wani da aka gano da suna Habibu Alhaji Ahmadu, wanda aka fi sani da “Munyaye,” daga ƙaramar hukumar Ikara, tare da bindigogi biyu kirar revolver ƙirar gida.
Ya amsa cewa ya taba kai hari ga wani mazaunin yankin, kuma an danganta shi da wata ƙungiyar ’yan ta’adda da ke aiki a yankin.
Kazalika, rundunar ta ce an kuma kai wani samamen a ranar hudu ga watan na Oktoba a kauyen Gazara da ke ƙaramar hukumar Makarfi, inda aka kama mutum 14, ciki har da wani Bello Umar, wanda aka taɓa gurfanar da shi a baya kan laifin garkuwa da mutane.
Dukkan waɗanda aka kama suna tsare a hannun ’yan sanda yayin da ake ci gaba da bincike.
Rundunar ta ce tana ci gaba da farautar sauran mambobin ƙungiyar da kuma ƙoƙarin kwato ƙarin makamai.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link
Leave a Reply