Gwamnati Ta San Sunaye Da Wuraren Da ‘Yan Ta’adda Suke — Sheikh Gumi

[ad_1]

Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya ce Gwamnatin Nijeriya ta san sunaye da kuma wuraren da ‘yan ta’adda ke ɓoye a ƙasar.

Malamin ya bayyana hakan ne yayin wata hira da ya yi da DRTV, inda yake mayar da martani kan zargin cewa yana da alaƙa da ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda a yankin Arewa maso Yamma.

  • Ramadan: ‘Yansanda Sun Buƙaci A Sanya Ido A Kano A Goman Ƙarshe
  • Kamfanonin Kasa Da Kasa Sun Nuna Gamsuwa Da Dimbin Damarmakin Da Kasuwar Kasar Sin Ta Samar

A cewarsa, gwamnati na da cikakken bayanai game da ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai.

“Gwamnati ta san kowane ɗan ta’adda da sunansa da kuma inda yake,” in ji Gumi.

Ya kuma kare kansa kan ganawar da ya taɓa yi da ‘yan bindiga, yana mai cewa bai taɓa zuwa tattaunawa da su shi kaɗai ba.

Ya ce yawanci yana zuwa ne tare da jami’an tsaro kamar ‘yansanda da sojoji, sannan a wasu lokuta tare da sarakuna.

Gumi, wanda tsohon likita ne kuma tsohon kyaftin a rundunar sojojin Nijeriya, ya sha bayyana cewa tattaunawa da ‘yan bindiga na iya taimakawa wajen kawo ƙarshen matsalar tsaro, maimakon dogaro da ƙarfin soji kawai.

Har yanzu gwamnatin tarayya da jami’an tsaro ba su fitar da wata sanarwa ba kan wannan iƙirari nasa.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *