Gwamna Abba Ya Sauke Shugaban Ma’aikatan Kano Daga Muƙaminsa
[ad_1]
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sauke Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin jihar, Abdullahi Musa, daga muƙaminsa.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar da yammacin ranar Talata.
- Cinikin Kasar Sin a Watanni 2 Na Farkon Bana Ya Karu Da 18.3% Idan Aka Kwatanta Da Na Shekarar Da Ta Gabata
- Jami’an Tsaro Sun Kashe ‘Yan Bindiga 5 A Jihar Zamfara
Sanarwar ta ce an ɗauki matakin ne a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin gwamnati na inganta aikin ma’aikatan gwamnati a jihar, domin ƙara inganci, bin doka da kuma kyautata ayyukan da suke yi wa jama’a.
Gwamnan ya gode wa tsohon Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin bisa gudunmawar da ya bayar da kuma jajircewarsa wajen yi wa Jihar Kano hidima a lokacin da yake kan muƙaminsa.
Haka kuma, gwamnan ya umarci Hajiya Bilkisu Shehu Maimota, wadda ke riƙe da muƙamin Babbar Sakatare mai kula da harkokin gudanarwa da ayyuka a Ofishin Majalisar Zartarwa, da ta riƙe muƙamin Shugaban Ma’aikatan Gwamnati na riƙon ƙwarya har sai an naɗa wanda zai maye gurbin.
Sanarwar ta kuma ƙara da cewa an umarci Abdullahi Musa da ya miƙa ragamar ofishin ga mai riƙon muƙamin kafin ko a ranar Laraba, 11 ga watan Maris, 2026.
[ad_2]
Source link