’Yan bindiga sun harbi Mataimakin Kwamshin ’yan sanda a Jigawa
[ad_1]
Wani Mataimakin Kwamishinan ’Yan Sandan ya tsallake rijiya da baya da raunin harbi a wani harin kwanton bauna da ’yan bindiga suka kai wa wata tawagar ’yan sanda a Jihar Jigawa.
Rundunar ’yan sandan jihar ta ce, ACP Kundi Dauda Abubakar, wanda shi ne kwamandan tawagar ya ji raunin harbin kibiya ne a yayin harin da aka kai muusu a yayin wani sumame da suka kai kan a maboyar ’yan bindiga a yankin Atuman Fulani da ke Karamar Hukumar Jahun a safiyar ranar Litinin ranar 21 ga Disamba, 2025.
Jami’an sun kai samamen ne bayan samun bayanan sirri kan ’yan bindigar da ake zargi da kai wa ’yan sanda hari a yankin Aujara da ke Jahun, a ranar 25 ga Nuwamba, inda suka dauke bindigar ɗaya daga cikin jami’an.
“Bisa bayanan sirri, tawagar ’yan sanda ƙarƙashin jagorancin ACP Kundi Dauda Abubakar ta kai farmaki kan ’yan bindigar a maboyarsu da ke Atuman Fulani,” in ji majiyar.
Ya ce da isowar ’yan sanda, ’yan bindigar suka yi kwanton bauna tare da fara harba kibiyoyi a kansu.
“ACP Kundi Dauda Abubakar ya samu rauni sakamakon harbin kibiya. Nan take aka garzaya da shi Babban Asibitin Jahun, inda aka yi masa magani, kuma a halin yanzu yana cikin ƙoshin lafiya,” a cewar majiyar.
Majiyar ta bayyana cewa a lokacin musayar wuta, ’yan sanda sun harbi biyu daga cikin ’yan bindigar, sai dai sun tsere da raunukan harsashi.
Haka kuma, jami’an tsaro na ci gaba da ƙoƙarin gano ’yan bindigar da suka gudu tare da ƙwato bindigar da aka sace a baya.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link