Yadda aka gudanar da bikin Kirsimeti a Katsina

[ad_1]



A yayin da Kiristoci ke shagalin bikin Kirsimeti a wannan rana, wakilin Aminiya a Jihar Katsina ya nemi jin ra’ayoyin wasu Kiristocin akan yadda suke kallon wannan biki.

Musamman a cikin jihar baki ɗaya kasancewar babu saƙon da ba za a rasa kiristocin da ke zaune a cikin su ba.

Tattaunawar Aminiya da wasu Mabiya Kirista

Mista Izrel ya ce, “muna gudanar da bikinmu cikin kwanciyar hankali babu wata damuwa. Nan cikin garin Katsina aka haife ni har na girma na kuma je garin mu na yo aure, amma ban taɓa ganin an nuna mani wariyar addini ba.

Ina zaune cikin jama’ar da suke ba addinin guda ba, amma kamar yadda muke zaune da su in mun gaiyace su suna zuwa. Kuma duk kayan abincin da muke yin amfani da shi don wannan rana a wajen su muke saye.

Idan zamu yi yanka dabbar su muke ba su yanka kuma ba su karɓar kuɗi don wannan aikin. Gaskiya ina cikin farin ciki sosai.

Ita kuwa Maman Blessing cewa tayi, inma har akwai wani abin damuwa a wannan biki na bana bai wuce rashin kuɗi ba.

“Ina sayar da abinci, amma wani lokaci sai mu koma da shi gida domin babu ciniki. Wannan shi ne babbar matsalar da wannan bikin wannan rana ya fuskanta. Amma zaman mu da Musulmi lafiya lau bamu da wata matsala. Ai mafi yawan gidajen da muke zaune na Musulmi ne, amma ko kuɗin haya yadda ‘yan-uwan su ke biya haka muke biya. Yanzu ma kaga yadda muke ta harkokin wannan rana, amma babu wanda ya damu da abin da muke yi sai ma taya mu murnar da wasu ke yi”.

Samuel, wanda ya ce yana zaune kusa da wani masallaci kuma ana wa’azi, amma bai taɓa jin malamai na sukar addinin kirastanci ba.

Kullum maganar haɗa kai ake yi tunda dukkan mu masu littafi ne, illa kawai wasu bambance na imani da yarda da muke da shi.

Tattaunawa da malamin addinin Musulunci

Da wakilin mu ya tuntuɓi wani malamin addinin Musulunci wanda ya nemi a sakaya sunan shi ya ce, babu wani wuri a cikin addinin Musulunci inda ya hana a yi wata walima don nuna farin cikin faruwar wani abu.

“Su ma ai tamkar walima ce suke yi don murnar wannan rana da suka yi imani da cewar ita ranar da aka haifi Annabi Isa, duk da cewar har a cikin su Kiristocin akwai waɗanda ba su yi imani da haka ba.

Sannan abin da zamu lura da shi a nan shi ne, in sun gaiyace mu wajen wata hidima har suka kawo abinci muna iya ci.

Illa irin na wannan rana ne aka hana Musulmi cin abincin da aka yi domin wannan dalilin. Amma hakan bai hana wanda ya ɗauka cewar zai ci abincin ba don manufar da aka yi shi ba”


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *