HOTUNA: Mabiya Shi’a a Najeriya na zanga-zangar goyon bayan Iran
[ad_1]
Magoya bayan ƙungiyar Islamic Movement of Nigeria wadda aka fi sani da shi’a, na ci gaba zanga-zangar goyon bayan Iran a yayin da take fuskantar hare-haren Amurka da Isra’ila.
IMN ƙarƙashin jagorancin Sheikh Ibrahim Zakzaky, ta ce mabiyanta sun gudanar da zanga-zangar a biranen Abuja da Zariya da Illela da Kaduna da Kano da Jigawa da Bauchi da Azare da Potiskum da Minna da Katsina da Yola da sauransu.
An kuma gudanar da zanga-zangar lumana a Jihar Legas, da ke kudu maso yammacin Najeriya, inda masu zanga-zangar suka ratsa wasu sassan yankin Maryland, ɗauke da alluna da tutoci, suna allawadai da abin da suka kira mamaye Iran da kuma kisan gilla kan jagoranta wanda ya daɗe yana mulki.
Zanga-zangar ta Legas na zuwa ne bayan irin zanga-zangar da mabiya Shi’ar suka gudanar a jihohin Kano da Yobe da Gombe da Bauchi a ranar Lahadi.
Ƙungiyar ta ce ta gudanar da addu’o’in neman nasara ga Iran, tana kuma jajanta wa al’ummar Musulman duniya, musamman Iraniyawa kan mutuwar jagoran addinin ƙasar, Ayatollah Sayyid Ali Khamenei.
An kashe Ayatollah Ali Khamenei ne a safiyar Asabar, 28 ga Fabrairu, a hare-haren haɗin gwiwa da Amurka da Isra’ila suka kai tare da wasu manyan jami’an gwamnatin Iran.




Masu alaƙa
[ad_2]
Source link