Duniya Na Bukatar Kasar Sin Fiye Da Kowane Lokaci
[ad_1]
Wasu nazarce-nazarce da jaridar Politico da kamfanin tsara nazarin ra’ayin jama’a na Public First suka gudanar a baya bayan nan sun gano cewa, mutane a kasashe 4 dake zaman manyan kawayen Amurka wato Canada da Jamus da Faransa da Birtaniya, suna ganin Sin a matsayin abar dogaro, wadda za ta iya taka ingantacciyar rawa a karni na 21.
Ba a wadannan kasashe ba kadai, farin jinin kasar Sin yana ta karuwa a duniya tsakanin kasashe daban-daban musamman a nahiyar Afrika da kudu maso gabashin Asia da sassan Latin Amurka da sauransu.
Kuma menene dalili?
Kai ya waye, ido ya bude, kowace kasa na son ta ga ta ci gaba, ta samu habakar tattalin arziki kuma ta tsaya da kafarta. Kuma wannan ita ce sabuwar dabarar da Sin ta bullo da ita a hadin gwiwar kasa da kasa, watau cin moriyar juna, hadin gwiwa cikin adalci da girmama juna ba tare da sharudda ko tsoma baki cikin harkokin wasu ba, sabanin yadda aka saba gani da ma yadda har yanzu wasu ’yan tsiraru ke neman danne tasowar kasashe da yin fatali da dokokin kasa da kasa da amfani da karfi domin wadata kansu.
A lokacin da ake bukatar hadin gwiwa da taimakekeniya tsakanin kasa da kasa, kasar Sin ta kara bude kofarta, tana kira ga kasashe su shigo su ci gajiyar ci gaban da ta samu da babbar kasuwar dake gare ta. Kowa yana son sauki, kuma kasar Sin ta gabatar da hakan ga kasashen duniya maimakon yadda wasu ke kara tsananta kulle kofa da tsaurara matakan cinikayya.
Idan ana magana ta ci gaba, to kowa ya san kasar Sin ta yi gaba sosai. Misali abubuwan da yanzu duniya ke mayar da hankali kan su, kamar kirkire-kirkiren fasahohin zamani da ayyukan masana’antu da makamashi mai tsafa da sauransu, duk kasar Sin ce jagora a wadannan bangare. Kuma ta sha fadi cewa, ci gabanta ba zai taba zama barazana ba, sai dai ya zama dama ga sauran kasashe. Kuma hakan ne tun da dimbin kasashe sun ci kuma suna kan cin gajiyar ci gaban kasar Sin. Wannan dalili ne ya sa shugabannin Turai suka yi ta kawo ziyara kasar Sin domin yanzu kowa ya san cewa, babu wanda zai iya dogaro da kansa shi kadai wajen samun ci gaba, haka kuma, duniya na bukatar kasar Sin.
Idan kuma muka yi la’akari da rikice-rikicen da suka addabi duniya, za mu ga cewa, Sin tana adawa da su. Kuma har kullum, burinta shi ne warware rikice-rikice ta hanyar lumana, kana a girma ’yancin dukkan kasashe ba tare da la’akari da girmansu ba.
Wadannan dalilai kalilan, na daga cikin irinsu masu tarin yawa da suka yi daidai da burin kasa da kasa da al’ummominsu a zamanin da muke ciki, kuma su suka sa kima da daraja da farin jinin Sin ke karuwa a idanun duniya, domin tana da karfin tabbatar da burin kasa da kasa na samun zaman lafiya da ci gaba na bai daya a duniya. (Faeza Mustapha)
[ad_2]
Source link