An kama wata uwa kan binne jaririyarta a Kebbi
[ad_1]
’Yan sanda a Jihar Kebbi sun kama wata matashiya mai shekara 20, Maryam Atiku, bisa zargin binne jaririyar da ta haifa da ranta a unguwar Nasarawa da ke Kamba a Karamar Hukumar Dandi.
Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar, CSP Nafi’u Abubakar, ya fitar a wannan Larabar.
Ya ce matashiyar bayan ta haifi jaririyar, ta naɗe ta a cikin wasu zannuwan atamfa guda uku, sannan ta kai ta wani daji da ake kira Malam Yaro a yankin Nasarawa, inda ta tono rami ta binne ta da ranta.
Sai dai a cewar kakakin ’yan sandan, wani manomi mai suna Alhaji Kabiru Muhammad da ya fita aiki a gonarsa da ke kusa da Malam Yaro, ya lura da alamun an tona wani wuri da ya yi kama da ɗan ƙaramin kabari.
Hakan ce ta sanya manomin ya yi kururuwar neman a kawo masa agaji, inda mutane suka taru aka taimaka har aka tono jaririyar da ranta.
Aminiya ta ruwaito cewa an dai garzaya da jaririyar Asibitin Gwamnati na Kamba, inda aka duba lafiyarta aka tabbatar tana cikin ƙoshin lafiya.
Sanarwar ta ce tawagar ’yan sanda daga sashen binciken manyan laifuka na SCID da ke Birnin Kebbi, ta kama matar nan take, kuma ana titsiye ta a yayin bincike ta amsa laifin, wanda babu wata-wata aka gurfanar da ita a kotu.
Kwamishinan ’yan sanda na jihar, CP Bello M. Sani, ya yaba wa matar gwamnan Kebbi, Hajiya Zainab Nasare Nasir Idris, bisa alawashin da ta sha na ɗaukar nauyin kula da jaririyar.
Haka kuma, ya gode wa manomin, Alhaji Kabiru Muhammad bisa irin rawar da ya taka wajen ceto jaririyar.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link