Erdogan ya yi kira da a kawo ƙarshen zubar da jini a Iran
[ad_1]
Shugaban ƙasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, ya yi kira da a kawo ƙarshen abin da ya bayyana a natsayin “zubar da jini” a Iran, yana mai jaddada aniyar ƙasarsa ta taimakawa wajen cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Amurka, Isra’ila da Iran.
Erdogan ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi ga mambobin jam’iyyarsa a Ankara a yammacin ranar Litinin.
“Za mu tsaya a ɓangaren zaman lafiya. Muna son a kawo ƙarshen zubar da jini, hawaye su daina zuba, kuma yankinmu ya samu dawwamammen zaman lafiya da ya shafe shekaru yana nema.”
Shugaban na Turkiyya, wanda ke da kyakkyawar alaƙa da Shugaban Amurka Donald Trump duk da yawan sukar da yake yi wa ƙawarta Isra’ila, ya ce hare-haren haɗin gwiwar Amurka da Isra’ila da aka kai a ranar Asabar—waɗanda suka haddasa yaƙin tare da janyo martanin ramuwar gayya daga Tehran—ba su dace da dokokin ƙasa da ƙasa ba.
“Za mu ƙara dagewa wajen tuntuɓar kowane ɓangare har sai an tsagaita wuta kuma an dawo da kwanciyar hankali a yankinmu,” in ji shi.
Erdogan ya ƙara da cewa yana cikin alhini ganin yadda fararen hula da yara waɗanda ba su ji ba ba su gani ba ke shan wahala sakamakon rikicin da ya ɓarke a Iran.
Turkiyya, wadda mafi yawan al’ummarta Musulmi ne kuma mamba a ƙungiyar tsaro ta NATO, na da iyaka mai tsawon kusan kilomita 500 da Iran.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link