’Yan bindiga sun kashe basarake, sun tarwatsa mutane a Sakkwato

[ad_1]



Wasu ’yan bindiga da ake zargin Lakurawa ne, sun kai hari ƙauyen Sayinna, da ke Ƙaramar Hukumar Tangaza a Jihar Sakkwato.

Sun kashe Hakimin ƙauyen, Malam Murtala Sa’adu, tare da wani mutum mai suna Ibrahim Mai-Kuɗi.

Mai bai wa shugaban Ƙaramar Hukumar Tangaza shawara, Alhaji Gazali Raka ne, ya tabbatar da harin.

Ya ce maharan sun kashe hakimin ne saboda yana taimaka wa ’yan sa-kai wajen tsaro a yankin.

An ce maharan sun shiga ƙauyen ne da misalin ƙarfe 1:30 na daren ranar Alhamis, inda suka dinga harbi a ko ina.

Bayan sun kashe mutanen biyu, sai suka tsere zuwa cikin daji.

Sojojin Operation FANSAN YANMA sun isa yankin, inda suka ɗauki gawarwakin zuwa asibiti.

Rahotanni sun nuna cewa Lakurawa sun kai hare-hare a wasu ƙauyuka na ƙananan hukumomin Kebbe da Tambuwal, inda suka ƙone gidaje, suka kwashe kaya, kuma suka tilasta mutane yin gudun hijira.

A ƙaramar hukumar Kebbe, ƙauyuka kamar Fakku, Sha’alwashi, Tulluwa, Bashi Bakin Dutse da Rafin-Gora sun zama kufai saboda mutane sun tsere.

Hakimin Fakku da iyalansa sun bar garin, sun tsere zuwa Koko a Jihar Kebbi, inda suka haɗu da ɗaruruwan ’yan gudun hijira daga yankin.

Matsalar tsaro a Jihar Sakkwato na ƙara ta’azzara, kuma jama’a na kira gwamnati ta ɗauki matakan gaggawa don kawo ƙarshen lamarin.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *