Dokar Haraji Na Fuskantar Turjiya
[ad_1]
An fara nuna damuwa a kan zargin da ake yi na yin wani abu da ya yi kama da zamba ko rainin hankalin da aka yi lamarin da ya shafi dokokin haraji da majalisun biyu na kasa suka yi, hakan ya biyo bayan turjiyar da wadansu ‘yan majalisa biyu suka yi dangane da yadda dokokin da gwamnati ta amince dasu suka zama doka aka yi masu wata kwaskwarima.
Jaridar Daily Trust ta bayyana wani rahoton yadda dan majalisar Wakilai ta kasa, Honorabul. Abdulsammad Dasuki dan jam’iyyar (PDP daga Jihar Sakkwato),ya gabatar da maganar a zauren majalisar, inda ya yi zargin cewa da akwai bambanci tsakanin kudurorin da su ‘yan majalisar suka amince da su a majalisun na kasa da kuma wadanda aka maida su suka zama doka har mutane suka fara ganin yadda suke.
- Xi Ya Jagoranci Taron Shugabannin JKS Dangane Da Kiyaye Ka’idojin Jam’iyya Da Yaki Da Cin Hanci
- Kasar Sin Ta Yi Tasiri Sosai Wajen Bunkasar Sashen Fitar Da Hajoji A Duniya
Da ya tashi zai yi magana a karkashin tsari na shida, dokar majalisar ta biyu daga cikin dokokin da suka shafi wani abin da ya kamata ayi magana a kan shi, Dasuki ya shaida wa majalisar cewa, an bata ma shi wata dama da yake da ita a matsayinsa na dan majalisar, inda ya dage da cewa su dokokin da suke kunshe a kundin dokokin harajin, ba irin wadanda suka tattauna bane a zauren majalisar, aka kuma kada kuri’a kansu da kuma amincewa da su a zauren majalisar.
Da yake hira da sashen Hausa na BBC a shirin shi na Ra’ayi Riga, Hoorabul Muhammad Bello Fagge (mai wakiltar mazabar gwamnatin tarayya ta Fagge, Jihar Kano) tare da Honorabul. Yusuf Shitu Galambi (mazabar gwamnatin tarayya ta Gwaram, Jihar Jigawa), cewa ya yi ko jan kunne kan cewa irin bambancin da aka samu na iya sa su rena wata dokar tsarin mulki, irin hakan kuma ya kara sa su mutane ba za su ci gaba da gani da kimar gwmnati ba ballantana ma su bi ita dokar da ta yi.
Honorabul. Fagge ya ce da farko an nuna rashin amincewa da su kudurorin saboda adawa da su, shi irin matakin ne har ya kai sa wa sai da aka tuntubar wasu mutane da kungiyoyi kafin a kai ga amincewa da su kudurorin a majalisun biyu.
“Domin mu a cikin mu dake daga jam’iyyun adawa da farko mun yi wata turjiya ne daga ita dokokin harajin da ake shirin samarwa saboda irin tsoro da shakkun da muke dasu cewa akwai wasu lamurran da za’ a iya shigarwa, ba tare da an masu cikakken bincike da tattauna abubuwan da ka iya faruwa a gaba.Irin hakan ne ya sa shi Shugaban majalisar Wakilai ta kasa, Tajudeen Abbas, ya kafa kwamitin da ya shiga sako da lungu na kasa, ya samu ganawa da Sarakunan gargajiya da kuma gwamnoni, domin samun irin gudunmawar da suka ba da da ta hada da wuraren da suke ganin, da akwai gyara da kuma shawarwarinsu zuwa ga su majalisun na kasa. Bayan da aka yi amfani da shi matakin, sai aka samu daidaito na su dokokin aka amince da su jamar yadda ya ce,’’.
Fagge ya ce an fara samun ta da jijiyar wuyan ne bayan da aka lura cewa ashe ma har su dokokin harajin da majalisun suka amince da su, sun bambanta da wadanda ita gwamnati ta yi amfani da su a matsayin dokokin harajin da gwamna ti amince ayi amfani da su.
Dan majalisar ya ce da akwai wadansu wurare da suka lura cewa an dauke aikin majalisa, da bangaren shari’a aka maida abin zuwa majalisar zartarwa, musamman ma hukumar tara haraji ta kasa.
Shi ma da yake tofa aibarkacin bakinsa a shirin na Ra’ayi Riga, Horabul. Galambi ya ce abin da ya sa ‘yan Nijeriya suke dari- dari da lamarin na shi harajin bai wuce rashin amincewa da yadda gwamnati ta ke kashe kudaden al’umma ba.
“Mun san da cewar mutane basu amince da maganar haraji ba saboda basu laminta ko amincewa gwamnati tana amfani, da kashe kudadensu wuraren da abin zai amfane su.Sai dai kuma idan har mutane basu wani shakku ko wata fargaba su na kuma yakini cewa gwamnati tana kan tafarki madaidaici, babu wanda zai yi shakkun cewa da akwai Lauje cikin Nadi kamar yadda ya bayyana,’’.
Galambi ya bayyana zargin da ake na an yi aringizon wadansu abubuwa da basu cikin kudurorin da suka amince su zama dokokin haraji, duk da yake da su majalisun na kasa basu yi cikakken binciken sanin yadda lamarin yake, domin kuwa su majalisun kasa sun kafa kwamitin da zai binciki yadda lamarin yake.
Ya yi kira da gwamnati da ta bar maganar fara amfani da dokokin na haraji da aka shirya za’a fara amfani da su watan Janairu na shekarar 2026 har sai shi kwamitin da aka kafa ya kammala binciken sa.
“Idan an gano cewar akwai wuraren da aka yi coge,sai an maido da abi zuwa majalisa ayi gyara a kuma bi kan ka’idar dokkin da ita majalisar tamince da su. Idan ba a gano wata matsala ba sai a fara amfani da su dokokin kamar yadda Galambi ya bada shawarar.
Ya ma nuna matukar damuwa a wurin da aka bahukumar tara kudade ta kasa ta daukai matakin tilastawa ba tare da umarni kotu ba,wannan ya saba abinda majalisar ta amince da ayi.
“Ya ce lamarin tilastawa ana yin sa ne da umarnin Kotu. Idan har an cire amincewar Kotu, hakan zai iya kawo tashin hankali a kasa abinda zai sa mutane ba za su amince da hakan ba kamar yadda ya furta”.
‘Yan majalisar sun ce kwamitin yana da mako hudu domin ya duba zargin da aka yi,su kuma bada shawarwari, inda ya ja hankali da tunatarwa cewa an amince ne da lamarin dokokin haraji bayan da aka tuntubi wadanda suka kamata aji ta bakin su, suka kuma bada shawarwari sannan aka tabbatar da cewar shawarwari zasu amfani ‘yan Nijeriya da yawancinsu Talakawa ne.
Jaridar Daily Trust ta bada rahoton cewa Shugaban majalisar Wakilai ta kasa, Tajudeen Abbas, ranar Alhamis ta makon da ya gabata ne ya kafa kwamitin da ya kunshi mutum bakwai domin ya yi bincike kan zargin da ake yi da yake nuna an yi aringizo domin gano bambnace- bambance da suke tsakanin kudurorin dokar haraji da majalisun suka amince da su, daga karshe kuma aka maida su suka zama dokar kasa.
Kwararru sun yi gargadi kan irin hadarin da yake tattare da sab akin bangaren zartarwa
Da yake bada ta shi gudunmawar a cikin shirin da Sashen Hausar ya yi,mai fashin baki kan lamurran da suka shafi tattalin arziki, Farfesa. Muttaka Usman, yace shi sha’anin haraji ba kawai ya tsaya kan abinda ya shafi haraji bane, akwai ma maganar tabbatar da ana amfani da shi ne domin bunkasa tattalin arziki da kuma kyautata jin dadin ‘yan Nijeriya.
Ya yi karin haske kamar haka “Haraji ba kawai ya tsaya kan sha’anin samun karin kudade bane, amma yadda za’ayi amfani da shi a bunkasa tattalin arziki da kuma jin dadin ‘yan Nijeriya gudunmawar sa ke nan lokacin shirin,”.
Ya kara cewa ana iya samun rashin amincewa da yadda gwamnati take tafiyar da lamurranta lokacin da tsare- tsare da manufofin da tace za ta yi suka sha bamban da abubuwan da take aiwatarwa.
“Farfesa Usman ya yi karin haske ami nuna ana iya samun takun saka da gwamnati saboda wasu lokutta abubuwan da gwamnati ta yi alkawarin yi, suna shan bamban da wadanda take yi.
Da yake sa albarkacdin bakinsa bayan ya yi nazarin kundin dokar ya kuma gano bambanci tsakanin dokokin da majalisun kasa suka amince da wadanda ita gwamnati amince su zama dokokin zaben na kasa, Farfesa kan harkar shari’a Auwalu H. Yadudu, cewa ya yi su bambance- bambancen da ake zargin akwai su, suna iya zama wata barazana kan tsarin mulki n da za’a tafiyar da gwamnati.
Ya ce irin wannan lamari ba alkhairi domin ba wata maganar ci gaba”domin kuwa ana iya samun wasu daga cikin majalisar zartarwa na iya wasu gyare- gyaren dokokin ba tare da amincewar ‘yan majalisa ba.
“Ta yayya mutum zai iya bayani kan kudurorin dokokin da aka dauki lokaci mai tsawo ana tattaunawa kan su, kai har ma sauraren ra’ayoyin jama’a aka yi, aka kuma amince da hakan, yanzu kuma ace an kara wasu abubuwa ko kuma gaba daya an cire wadanda aka amince da su wannan tambaya ce ya yi?”.
Ya tabo wuraren da suke da amfani kan dokar haraji ta Nijeriya, da ta hada da tanaje- tanajen da aka yi wa kudaden shigar da ake samu ta man fetur da kuma harajin sayen kaya, abinda ya ce yanzu bai dauke da abubuwan da ‘yan majalisar suka amince da su, su kasance cikin dokokin na haraji.
Martanin Kungiyar Lauyoyi
Kungiyar lauyoyin ta Nijeriya (NBA), ta bukaci gwamnatin tarayya da ta dakatar da aiwatar da dokokin haraji, har sai al’umma sun gamsu da aiwatar da tsarin.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, shugaban kungiyar lauyoyin na Nijeriya (NBA), Mazi Afam Osigwe, SAN ya ce; rigingimun da suka taso game da dokar gyaran haraji, na bukatar lura da gaskiya, amana da kuma aiki tare da bin tsarin dokokin Nijeriya.
LEADERSHIP ta rawaito cewa, a ranar Larabar da ta gabata, wani dan majalisar wakilai, Hon. Abdulsammad Dasuki na jam’iyyar PDP daga Jihar Sakkwato, ya gabatar da wani batu a zauren majalisar, inda ya ce; an samu sabani tsakanin dokokin haraji da majalisar dokoki ta kasa ta amince da su da kuma nau’ikan da aka gabatar da kuma bayyana wa jama’a.
Tun daga wancan lokaci, jam’iyyun siyasa, kungiyoyin farar hula (CSOs) da sauran ‘yan majalisa suka yi kira da a dakatar da dokar harajin, sakamakon rashin bin ka’ida.
Duk da haka, kungiyar lauyoyin ta kasa ta yi kira ga dukkanin hukumomin da abin ya shafa, da su yi hanzari tare da gaggawa, domin magance wannan takaddama, “a cikin manyan hanyoyi na moriyar tsarin mulki, akwai samun kwanciyar hankali a bangaren tattalin arziki da kuma kiyaye doka”.
Sanarwar ta ce, “Wadannan abubuwan da ke faruwa, sun shafi tushen tsarin mulki, sannan kuma suna sanya ayar tambaya kan tsattsauran ra’ayi, wanda dole ne a yi la’akari da doka, musamman a tsakanin al’ummar da suka rungumi dimokuradiyya.
[ad_2]
Source link