Dalilin da ya hana mu gurfanar da El-Rufai a Kotu — EFCC

[ad_1]



Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Ƙasa (EFCC) ta bayyana dalilin da ta ce shi ne ya sa har yanzu ba ta gurfanar da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El‑Rufai, gaban kotu ba, duk da an yi masa tambayoyi tsawon kwana uku.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa (NAN) ya ruwaito cewa EFCC ta tsare El-Rufai na tsawon darare biyu daga 16 zuwa 18 ga Fabrairu, bisa zargin almundahana da aka danganta masa.

Wata majiyar hukumar EFCC ta shaida wa NAN cewa har yanzu bincike na gudana, don haka ba za a garzaya kotu ba sai an kammala binciken yadda ya kamata.

Majiyar ta ce zargi ne mai girma da nauyin gaske, saboda haka hukumar ba za ta yi gaggawa ba, sai ta gudanar da cikakken bincike cikin ƙwarewa kafin a gurfanar da shi.

“Har yanzu muna bincike kan tsohon gwamnan; ba mu kammala ba har zuwa lokacin da muka bayar da belinsa a ranar Laraba da ta gabata,” in ji majiyar.

Ta kara da cewa: “Ko da yake Hukumar ICPC ce ta karɓe shi nan take bayan mun sake shi, za mu ci gaba da bincike bayan ya kammala da ICPC.

“Da zarar mun kammala dukkan binciken, za mu kai shi kotu kan zarge-zargen da ake masa.”

Aminiya ta ruwaito cewa an soma tsare El-Rufai ne a ranar Litinin, 16 ga Fabrairu, bayan ya amsa gayyatar EFCC, sannan aka sake shi da daren Laraba, 18 ga Fabrairu, inda daga bisani Hukumar ICPC ta sake karɓarsa.

A wata sanarwa da mai magana da yawun tsohon gwamnan, Muyiwa Adekeye, ya fitar a ranar Talata, ya ce El-Rufai ya shafe kwanaki tara a hannun hukumomin yaƙi da cin hanci biyu.

Adekeye ya ƙara da cewa har zuwa ranar Litinin, lauyoyin El-Rufai ba su samu amsa daga ICPC kan bukatar belin da suka shigar masa ba, kuma hukumar ba ta nuna musu umarnin kotu da ke ba da damar ci gaba da tsare shi ba, duk da ƙarewar wa’adin sa’o’i 48 da kundin tsarin mulki ya tanada na tsare mutum ba tare da tuhuma ba.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *