NAJERIYA A YAU: Falalar Sallan Tarawih Ga Alummar Musulmi A Watan Ramadan
[ad_1]
Ƙarin Podcasts
A duk lokacin da watan azumin Ramadan ya kama, al’ummar Musulmi kan cika masallatai domin gudanar da sallar Tarawihi cikin karsashi da himma. A kwanakin farko, ana ganin sahu sun cika, zuciya cike da nishadi da kwadayin lada. Sai dai abin takaici, bayan wasu kwanaki, wasu kan fara ja da baya — wani saboda gajiya, wani saboda shagaltuwa da harkokin yau da kullum, ko kuma rashin juriya.
Wannan yanayi na nuna bukatar tunatarwa kan muhimmanci da falalar sallar Tarawihi, domin ita ba kawai karin ibada ba ce a watan Ramadan, illa wata babbar hanya ce ta neman gafara da kusanci ga Allah. Manzon Allah (SAW) ya karfafa tsayuwar dare a watan Ramadan, yana mai bayyana cewa duk wanda ya tsaya sallar dare cikin imani da neman lada, za a gafarta masa zunubansa na baya.
Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai duba ne kan falalar sallan tarawihi yayin da Musulmi ke cigaba da gudanar da azumin watan Ramadan.
Domin sauke shirin, latsa nan
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link