Kisan Ƙare Dangi: Sojojin Amurka Sun Fara Aikin Samar Da Tsaro A Nijeriya

[ad_1]

Kimanin jami’an sojan Amurka 100 tare da kayan yakinsu, sun isa filin jirgin saman Bauchi, domin tallafa wa sojojin Nijeriya a fannin horo da taimakon fasaha da kuma hadin gwiwar leken asiri, kamar yadda hedkwatar tsaro ta kasa ta sanar a ranar Litinin.

Daraktan yada labarai na tsaro, Manjo Janar Samaila Uba, a wata sanarwa da ya fitar ya ce; turo sojojin wani Bangare ne na hadin gwiwar tsaron Nijeriya da Amurka, biyo bayan tattaunawar da aka yi ta hadin gwiwa a kwanan baya tsakanin tawagogin sojojin kasashen biyu.

  • Jerin Sharuddan Da Chelle Ya Gindayawa NFF Domin Cigaba Da Jagorantar Super Eagles
  • Ramadan: Lokutan Buda-Baki Da Sahur Na Azumi Na 2

“Isowar jami’an Amurka, shiri ne na da gangan, bisa ga bukatar da gwamnatin tarayyar Nijeriya ta gabatar na neman tallafi wajen magance bukatu na horar da sojoji,” in ji hedikwatar

Ya kara da cewa, hadin gwiwar na nufin samar da damammaki na fasaha na musamman, don karfafa karfin Nijeriya na dakile barazanar ‘yan ta’adda da kuma kare al’ummomi masu rauni a fadin kasar.

Manjo Janar Uba ya jaddada cewa, ma’aikatan na Amurka, kwararru ne da ke aiki a fagen bayar da shawara da horarwa, ba sojojin yaki kawai ba ne, sannan kuma za a gudanar da dukkan ayyuka a karkashin iko da shugabanci da kuma kula da gwamnatin Nijeriya tare da hadin gwiwa da rundunar sojojin Nijeriya.

Hedikwatar ta kara da cewa, sojojin Nijeriya tare da masu bayar da shawara na Amurka, za su gudanar da atisayen horaswa na hadin gwiwa da tsare-tsaren hadin gwiwa da suka shafi leken asiri, wanda aka tsara domin inganta karfin sojojin da za su iya ganowa tare da dakile kungiyoyi masu tsattsauran ra’ayi da ke neman tada zaune tsaye a kasar.

“Rundunar Sojin Nijeriya na ci gaba da dagewa wajen yakar kungiyoyin ‘yan ta’adda da ke barazana ga daukacin tsaron kasa ‘yan kasar,” in ji sanarwar, tare da tabbatar wa ‘yan Nijeriya gaskiya da kuma bayanan da suka dace game da hadin gwiwar.

Trump ya ce, za a iya samun karin matakan sojan Amurka a Nijeriya, yayin da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa; tun a karshen watan Nuwamba ne, Amurka ta fara gudanar da zirga-zirgar jiragen sama a kasar daga Ghana.

Kisan Kare Dangi Na Kirista

Dangantaka tsakanin Nijeriya da Amurka ta sauya, bayan da Trump ya yi barazanar shiga Nijeriya a karshen shekarar da ta gabata, domin daukar fansar abin da ya kira da ‘kisan kare dangi na Kiristoci’.

Bayan ‘yan makwanni, a ranar Kirsimeti, jiragen ruwan yakin sojojin ruwan Amurka tare da taimakon jami’an leken asirin Nijeriya, sun harba makamai masu linzami na Tomahawk guda 16, a wani abin da Trump ya ce; ‘yan ta’adda ne ke da alhakin kashe Kiristocin Nijeriya.

Nijeriya dai, ta fuskanci matsanancin matsin lamba daga Amurka, a kan ta dauki mataki bayan Trump ya yi zargin cewa; kasar ta gaza wajen kare kiristoci daga ‘yan bindiga da ke zaune a yankin Arewa maso yamma.

Gwamnatin Nijeriya, ta musanta duk wani tsangwama ga kiristoci, tana mai cewa; tana kai wa ‘yan ta’adda da sauran kungiyoyi masu dauke da makamai hare-hare tare da kashe Kiristoci da Musulmai.

Rundunar sojin Amurka da ke da alhakin gudanar da ayyukanta a Afirka, rundunar sojin Amurka da ke Afirka ta ce; tana taimaka wa Nijeriya a yakin da ke da kungiyoyi masu tsattsauran ra’ayi da suka hada da kungiyar Boko Haram da kuma yankin yammacin Afirka.

Shugaban JIBWIS ya bukaci gwamnatin tarayya da ta fayyace alakar sojojin Amurka da Nijeriya,

Shugaban Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Ikamatis Sunnah (Jibwis) ta Kasa, Abdullahi Bala Lau, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta yi watsi da yarjejeniyoyin da suka kulla da Amurka dangane da batun tura sojojin Amurka Nijeriya.

Da yake zantawa a wata hira da ya yi BBC Hausa, Bala Lau ya ce; kasancewar Amurka kasa ce ta duniya da ke da manyan hanyoyin leken asiri, ya kamata ta rika tantance bayanai game da Nijeriya, maimakon dogaro da labaran da suke kunshe da siyasa a ciki.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *