Gwamnatin Jigawa Na Ƙoƙarin Ganin DSS Ta Saki Walida — Umar Namadi

[ad_1]

Gwamnatin Jihar Jigawa ta ce tana yin duk abin da ya dace domin ganin an saki Walida Abdulhadi, yarinyar da ake zargin wani jami’in DSS da sace ta tare da tilasta mata ta sauya addini.

A wata sanarwa, gwamnatin ta ce tana ɗaukar lamarin da matuƙar muhimmanci saboda irin damuwar da ya jawo a cikin al’umma.

  • Haƙƙin Ɗan’adam Na Fuskantar Mummunar Barazana A Duniya – Guterres
  • Kwamitin Kolin JKS Da Majalisar Gudanarwa Ta Kasar Sin Sun Taya Tawagar Kasar Ta Wasannin Olympics Na Lokacin Hunturu Murna

Batun Walida ya janyo cece-kuce a faɗin Nijeriya, inda ƙungiyoyin fararen hula ke neman a yi mata adalci.

Rahotanni sun ce kotu ta umarci a sake ta domin a haɗa ta da iyayenta, amma har yanzu tana hannun DSS.

Gwamnatin ta ce ma’aikatar shari’a na aiki tare da hukumomi domin tabbatar da an bi doka kuma an kare haƙƙin yarinyar, yayin da gwamna da manyan jami’ai ke ci gaba da tuntuɓar masu ruwa da tsaki.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *