Chelsea Ta Naɗa Liam Rosenior A Matsayin Sabon Kocinta

[ad_1]

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Chelsea, ta sanar da nadin kocin Strasbourg Liam Rosenior a matsayin sabon kocinta da zai maye gurbin Enzo Maresca wanda ya bar ƙungiyar a makon jiya.

Kocin ɗan kasar Ingila, ya sanya hannu kan kwantiragin shekarun 6, yayin da zai jagoranci ƙungiyar har zuwa shekarar 2032.

  • ’Yan Bindiga Sun Kashe Mutum Ɗaya Daga Cikin Likitoci 2 Da Suka Sace A Edo
  • An Kama Mutane 3 Kan Ƙone Gidan Wata Mata A Kwara

Yayin da yake magana da manema labarai Lima ya ce wannan aiki da ya samu a Chelsea babbar dama ce a gare shi, kuma yana matukar alfahari da naɗin da aka yi masa.

“Wannan ƙungiya ce mai cike da tarihi, don haka zan so nima na rubuta nawa tarihin a Chelsea musamman na lashe kofuna”.

Ya ƙara da cewa, “Aikina shi ne na ƙara taimaka wa wannan ƙungiya domin cimma abin da take nema a kowane kofi da muke bugawa.”

Rosenior, mai shekaru 41, ya ce “wannan dama ce da ba zan taɓa ƙin amsa ba.”

Rosenior ya maye Enzo Maresca wanda ya raba gari da Chelsea bayan samun saɓani da mahukuntanta.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *