Zan bai wa Estevao damar samun nutsuwar ci gaba da murza leda — Rosenior

[ad_1]

Kocin Chelsea, Liam Rosenior, ya ce ba zai azzazzala wa ɗan wasan ƙungiyar Estevao dawowa ba bayan hutun tausayawa da jin ƙai da aka ba shi.

A bayan nan ne ƙungiyar ta bai wa ɗan wasa Estevao hutun komawa gida Brazil saboda wasu dalilai da aka bayyana na a matsayin na ƙashin kai da ɗan wasan yake buƙata a halin yanzu.

Da wannan ne kociyan ƙungiyar ya ce ba zai sanya wa ɗan wasan wa’adin dawowa ba har sai ya samu natsuwar ci gaba da murza leda.

A halin yanzu dai Estevao mai shekaru 18 zai rasa wasan daf da na ƙarshe na League Cup da Chelsea za ta fafata da Arsenal, yayin da Rosenior ya jaddada cewa nutsuwar zuciya da kwanciyar hankali na ɗan wasan sun fi komai muhimmanci.

Rosenior ya kuma ce sauye-sauyen ‘yan wasa na daga cikin salo da dabarunsa na jan ragamar ƙungiyar, la’akari da cewar Chelsea na fafatawa a gasanni da dama.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *