Gasar Kofin Duniya ta 2026 ita ce ta ƙarshe da zan buga — Ronaldo
[ad_1]
Fitaccen ɗan wasan ƙasar Portugal, Cristiano Ronaldo, ya tabbatar cewa Gasar Kofin Duniya ta shekarar 2026 ita ce ta ƙarshe da zai buga a rayuwarsa ta ƙwallon ƙafa.
Ronaldo mai shekaru 40, wanda ya ci ƙwallo fiye da 950 a matakin kulob da ƙasarsa, ya ce yana shirin yin ritaya nan da shekara ɗaya ko biyu masu zuwa.
“Eh, tabbas wannan shi ne Kofin Duniya na ƙarshe da zan halarta. Zan kai shekara 41, kuma ina ganin wannan ne lokacin da ya dace na ajiye takalmi,” in ji shi a wata tattanawa a Saudiyya.
Ronaldo, wanda yanzu ke bugawa kulob ɗin Al-Nassr ta Saudiyya, ya ce yana fatan cimma burin zura ƙwallo 1,000 kafin ya yi ritaya gaba ɗaya daga tamaula.
Tsohon ɗan wasan Manchester United, Real Madrid da Juventus, shi ne kan gaba a tarihin cin ƙwallo a matakin ƙasa, inda ya zura ƙwallo 143 a tawagar Portugal.
Ronaldo ya fara buga Kofin Duniya a shekarar 2006, lokacin da Portugal ta kai matakin kusa da na ƙarshe amma ta sha kashi a hannun Faransa.
A halin yanzu, zaƙaƙurin ɗan wasan bai taɓa lashe Kofin Duniya ba, sai dai ya taimaka wa ƙasarsa ta lashe Gasar Euro ta 2016 da kuma UEFA Nations League har sau biyu.
Yanzu haka, tawagar da Roberto Martínez ke jagoranta tana daf da samun gurbin shiga gasar ta 2026 da za a gudanar a Amurka, Kanada da Mexico, idan ta doke Jamhuriyar Ireland ranar Alhamis.
Ronaldo wanda ya zama ɗan wasan farko da ya ci ƙwallo mafi yawa a tarihin cancantar Kofin Duniya da ƙwallo 41 ya ce ritayarsa ba za ta zama abu mai sauƙi ba.
“Zai yi wuya sosai. Zan iya kuka ma, domin ni mutum ne mai buɗaɗɗiyar zuciya. Amma lokaci ya kusa,” in ji shi a wata hira da ya yi a shirin Piers Morgan Uncensored.
Ronaldo ya koma Saudiyya daga Manchester United a ƙarshen shekarar 2022, inda rahotanni suka nuna yana samun kusan euro miliyan 200 duk shekara.
A watan da ya gabata, mujallar Forbes ta bayyana shi a matsayin ɗan wasan da ya fi kowa samun kuɗi a duniya, yayin da jaridar Bloomberg ta tabbatar da cewa ya zama ɗan wasan ƙwallon ƙafa na farko da ya zama biloniya.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link