Floyd Mayweather zai dawo damben ƙwararru
[ad_1]
Fitaccen ɗan damben boksin na duniya, Floyd Mayweather ya sanar da cewa zai dawo fagen sana’arsa domin komawa gasar damben ƙwararru, bayan fafatawar nune-nune wato exhibition da zai yi da Mike Tyson a wannan bazara.
Mayweather mai shekaru 48, shi ne zakaran damben boksin ajin matsakaita nauyi na duniya wanda ya yi ritaya a shekarar 2017 ba tare da ya taɓa sha kaye ba a fafatawa 50 da ya yi.
Sai dai tun daga wancan lokacin, Mayweather ya ci gaba da shiga fafatawar nune-nune bayan ritayar da ya yi.
A wata sanarwa da ya bai wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP, Mayweather ya ce: “Har yanzu ina da ƙarfin kafa sabbin tarihi a damben boksin.
“Daga fafatawar da zan yi da Mike Tyson zuwa gasar ƙwararru ta gaba, babu wanda zai tara kuɗi, ya ja hankalin masu kallo a duniya, ko ya haifar da kuɗaɗe kamar yadda nake yi.”
Bayanai sun ce ana shirya fafatawar sa ta farko a matsayin ƙwararren ɗan dambe a wannan bazarar, inda za a bayyana abokin karawarsa da sauran bayanai nan gaba kaɗan.
Mayweather, wanda ake wa laƙabi da “Money”, wato “kuɗi” ya taɓa zama mai nishaɗantarwa mafi samun kuɗi a duniya, inda ya samu kusan dala miliyan 300 a shekarar 2015, a cewar Forbes.
A lokacin ganiyarsa, ana kallon sa a matsayin gwarzon boksin wanda ya mamaye ajin matsakaita nauyi tsawon fiye da shekaru goma.
Sai dai duk da nasarorin da ya samu, Mayweather ya jima yana fuskantar cece-kuce, inda wasu ke sukar salon dambensa na kariya fiye da kai hari, wasu kuma sun zarge shi da guje wa manyan abokan karawa domin ƙara wa tarihin sa kyau.
Haka kuma ya taɓa shiga gidan yari sakamakon wata matsala ta cikin gida da rutsa da shi.
Duk da haka, ƙarfinsa, jajircewa, ƙwarewa da basirarsa a boksin sun sa takwarorinsa na girmama shi a fagen dambe.
Fafatawar sa ta ƙarshe a matsayin ƙwararren ɗan dambe ita ce wadda ya yi a 2017, inda ya doke tauraron UFC Conor McGregor.
Daga baya ya ci gaba da fafatawar nune-nune, ciki har da nasarar da ya samu kan John Gotti III a Mexico a watan Agustan 2024, da kuma fafatawa da fitattun taurarin talabijin da ‘yan YouTube.
Rahoton mujallar damben boksin ta Ring Magazine ya ce fafatawar nune-nunen Mayweather da Tyson za ta gudana ne a ranar 25 ga Afrilu a Kongo, sai dai har yanzu ba a tabbatar da kwanan wata ko wurin a hukumance ba.
“Iron Mike” Tyson mai shekaru 59 ya shiga fagen daga na ƙarshe a watan Nuwamban 2024, inda ya sha kaye a hannun Jake Paul a Texas, a fafatawar da kamfanin Netflix ya ɗauki nauyi, wadda dubban mutane suka kalla kai tsaye, sannan miliyoyi suka kalla daga nesa a faɗin duniya.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link