Kafafen Yada Labarai Na Kasashen Waje: Taron Npc Da Cppcc Na Sin Za Su Samar Da Sababbin Damammaki Ga Duniya

[ad_1]

Kafafen yada labarai na kasashen waje sun ci gaba da bibiyar yadda taron majalisar wakilan jama’ar Sin NPC da taron majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta CPPCC ke gudana, kuma suna jinjinawa matakan da Sin ta dauka a fagagen kirkire-kirkire da fadada bude kofa ga ketare, inda suke ganin hakan zai samar da sababbin damammaki ga duniya.

Gidan rediyon kasa na Kenya ya wallafa wani labari a shafukansa na yanar gizo ya nuna cewa, a bana wadannan manyan taruka 2 sun fitar da wata alama a fili, wato kasuwar Sin a bude take. A ganin Kenya, ta hanyar yin hadin gwiwa da Sin, za ta iya inganta ababen more rayuwa, da kara ingancin kayayyaki da kuma kara kimar kayayyakin a duniya. Lamarin da zai kawo karin guraben ayyukan yi ga al’ummar Kenya, da karin kudaden shiga da kuma kwanciyar hankali.

Tashar Afirka ta gidan talabijin na BRICS na kasar Afirka ta Kudu ta ci gaba da watsa labarai kan ayyuka da dama na manyan taruka 2 na kasar Sin kai tsaye, inda take taimakawa masu kallo fahimtar yanayin ci gaban hadin gwiwar Sin da kasashe masu tasowa. (Amina Xu)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *