’Yan bindiga sun kashe jami’an NSCDC 8, sun sace ɗan China a Edo

[ad_1]



Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kai hari yankin Okpella, da ke Ƙaramar Hukumar Etsako ta Gabas, a Jihar Edo, inda suka kashe wasu jami’an tsaro.

Sun kashe jami’an Sibil Difens guda takwas sannan suka yi garkuwa da wani ma’aikacin ƙasar China.

Haka kuma, sun jikkata wasu jami’an Sibil Difens h6udu da wani mutum, waɗanda yanzu haka suna asibiti inda ake kula da ita.

Jami’an da lamarin ta shafa suna tsaron ma’aikatan ƙasar China na Kamfanin Simitin BUA.

Suna kan hanyarsu na zuwa wajen da suke aikin siminti lokacin da aka tare su a bakin kofar shiga kamfanin.

’Yan bindigar, ɗauke da makamai suka buɗe musu wuta inda suka kashe jami’ai takwas nan take.

Sun sace ɗaya aga cikin ma’aikatan ƙasar China, sauran huɗun an ceto su cikin ƙoshin lafiya.

Wani babban jami’in NSCDC ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya faru da misalin ƙarfe 10 na dare.

Yanzu haka hukumomin tsaro sun fara aikin haɗin gwiwa don bincike a dajin da ke kusa yanki , domin kuɓutar da wanda aka sace.

Kwamandan NSCDC na Jihar Edo, Gbenga Agun, ya ziyarci wajen da lamarin ya faru da kuma jami’an da suka jikkata a asibiti.

Mai magana da yawun hukumar a jihar, Efosa Ogbebor, ya ce ofishin hedikwatar hukumar ne kawai zai fitar da sanarwa a hukumance.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *