Kasar Sin Za Ta Karfafa Sabbin Masana’antu

[ad_1]

Ma’aikatar kula da masana’antu da fasahar sadarwa ta kasar Sin (MIIT), ta ce kasar Sin za ta aiwatar da jerin shirye-shirye da matakai da ke da nufin rayawa da karfafa sabbin masana’antu da wadanda za su bullo nan gaba.

A cewar ma’aikatar, za a aiwatar da shirye-shiryen ne yayin aiwatar da shirin raya kasa na shekaru biyar-biyar na 15 tsakanin 2026 da 2030.

Mataimakin ministan ma’aikatar Zhang Yunming ya shaidawa wani taron manema labarai a yau Laraba cewa, za a zurfafa kokarin neman sabbin abubuwan da za su ingiza ci gaban sabbin masana’antu da bunkasa amfani da sabbin fasahohin kera kayayyaki a sabbin yanayi da kafa cibiyoyin misali ga sabbin masana’antun.

Zhang Yunming ya kara da cewa, a fannin masana’antun da za su bullo nan gaba kuwa, kasar Sin za ta aiwatar da ka’idojin da za su yayata ci gaban kirkire-kirkire da bangaren ya samu da aiwatar da jerin ayyukan kimiyya da fasaha masu matukar muhimmanci da tallafawa hukumomin yankunan wajen raya irin wadannan masana’antu bisa yanayin da yankunan ke ciki, yana mai cewa, hukumomi za su kara amfana da asusun jari na gwamnati. (FMM)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *