Ba zan koma APC ba, ina nan daram a NNPP — Kwankwaso
[ad_1]
Jagoran Kwankwasiyya na Ƙasa, Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi watsi da kiranye-kiranye da wasu ke masa na ficewa daga jam’iyyar NNPP zuwa APC.
Wannan na cikin wata sanarwa da jagororin ƙungiyar Kwankwasiyya suka fitar bayan wani taro da suka gudanar a ranar Juma’a, 2 ga watan Janairu, 2026, a Kwankwasiyya House da ke titin Miller Road, Kano.
Sanarwar na ɗauke da sa hannun Magaji Mato Ibrahim (SAN), Mai Bai Wa Jam’iyyar NNPP Shawara a Harkokin Shari’a na Ƙasa.
Ƙungiyar ta yi watsi da duk wata magana ta sauya sheƙa, inda ta bayyana hakan a matsayin ƙarya.
Ta jaddada cewa irin waɗannan kiranye-kiranye ba su da alaƙa da aƙida da tsarin tafiyar Kwankwasiyya.
Ta bayyana cewa tafiyar Kwankwasiyya ba ta da alaƙa da duk wata sanarwa, jawabi ko rahoton kafafen yaɗa labarai da ke kira ga Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ko mambobin tafiyar su koma wata jam’iyya.
Ta kuma buƙaci jama’a da su yi watsi da irin waɗannan rahotanni.
Ƙungiyar ta ƙara da cewa wasu daga cikin mutanen da suka yi irin waɗannan kiranye-kiranye na iya yin hakan ne saboda rashin cikakken bayani ko matsin lamba daga wani waje.
Ta tabbatar da cewa Sanata Kwankwaso da dukkanin mabiya Kwankwasiyya suna nan daram a jam’iyyar NNPP.
Ta jaddada cewa ba a bai wa kowa umarni ko izinin yin kira ko yunƙurin ficewa daga jam’iyyar ba.
Game da rikicin shugabanci a jam’iyyar NNPP a Jihar Kano, ƙungiyar ta ce kwamitin gudanarwa na ƙasa na jam’iyyar (NWC) ya rushe shugabannin jam’iyyar na jiha, ƙananan hukumomi da kuma na mazaɓu.
Saboda haka, ta ce a halin yanzu babu wani sahihin shugabancin a kowanne mataki a Jihar Kano, kuma babu wanda ke da ikon yin magana ko aiki a madadin jam’iyyar.
Ƙungiyar ta kuma yi kira ga mabiya tafiyar Kwankwasiyya da su kasance masu natsuwa, ladabi da haɗin kai, tare da guje wa jita-jita.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link