Wata mata ta kashe ’yar shekara 7 a Ribas
[ad_1]
Ana fargabar cewa wata mata mai suna Success ta kashe wata yarinya mai shekaru bakwai, Alicia Olajumoke, a unguwar Rumueme da ke birnin Fatakwal na Jihar Ribas.
Mazauna yankin sun shaida wa Aminiya cewa matar da ake zargin tana da kusanci da dangin mahaifiyar yarinyar, wacce ita kaɗai ce a wurin iyayenta.
Bayanai sun ce ita ma matar ta caka wa kanta wuƙa a wuya bayan kashe yarinyar, kuma bayan an garzaya da duk su biyun asibiti, likitoci suka tabbatar da cewa sun riga mu gidan gaskiya.
Lamarin wanda ya faru a ranar Talata ya ɗimauta mazauna yankin, la’akari da zargin cewa matar ta kashe yarinyar ce a gidanta bayan ta je har makarantarsu ta ɗauko ta ba tare da izinin mahaifiyarta ba.
Jami’ar hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sanda a Jihar Ribas, SP Grace Iringe-Koko, ta tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ta fitar ranar Alhamis, inda ta ce an kai gawar yarinyar ɗakin ajiye gawa domin bai wa likitoci damar kammala bincikensu na kimiyya gabanin soma nasu binciken.
“Mun ziyarci wurin da abin ya faru, mun ɗauki hotuna, kuma an garzaya da su asibiti inda aka tabbatar da mutuwarsu.”
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link