Tinubu Da Shugabannin ECOWAS Sun Gudanar Da Taron Kan Juyin Mulki A Guinea-Bissau
[ad_1]
Shugaba Bola Tinubu da sauran shugabannin ƙasashen Yammacin Afrika sun gudanar da wani taron gaggawa ta Intanet a ranar Alhamis domin tattauna juyin mulki a Guinea-Bissau.
Sojoji sun kifar da gwamnati a ranar Laraba tare da tsare Shugaba Umaro Sissoco Embaló, sannan suka naɗa Janar Horta Nta Na Man a matsayin shugaban riƙon ƙwarya na shekara guda.
Tinubu ya halarci taron ECOWAS daga Abuja, inda shugabannin suka tattauna kan halin da ake ciki da matakan da ya dace ƙungiyar ta ɗauka, kasancewar ECOWAS na adawa da juyin mulkin soja.
Taron ya nuna damuwar ƙungiyar kan yawaitar juyin mulki a yankin, da kuma ƙoƙarinta na kare dimokuraɗiyya da tabbatar da zaman lafiya a ƙasashen Yammacin Afrika.
Tsohon shugaban Nijeriya, Goodluck Jonathan yana Guinea-Bissau lokacin da sojoji suka kifar da gwamnatin ƙasar.
[ad_2]
Source link