Ƙarancin gas na iya ta’azzara rashin wuta a Najeriya

[ad_1]



Rashin wutar lantarki a Najeriya na iya ƙara ƙamari yayin da kamfanonin da ke samar da gas suka rage adadin gas ɗin da suke bai wa tashoshin samar da wuta masu amfani da gas.

Tashoshin ne ke samar da mafi yawan wutar lantarkin da ake amfani da ita a ƙasar.

Hukumar da ke kula da sarrafa wutar lantarki (NISO), ta ce tashoshin wutar lantarki na buƙatar adadin yawan gas miliyan 1,629 a kullum domin su yi aiki yadda ya kamata.

Amma zuwa ranar 23 ga watan Fabrairu, 2026, adadin gas da ake samu ya kai kimanin miliyan 692 a kowace rana, wato ƙasa da rabin abin da ake buƙata.

Wannan ya haifar da yawaitar katsewar wuta a jihohi da dama tare da shafar harkokin kasuwanci da rayuwar jama’a.

Babbar Daraktar Ƙungiyar Kamfanonin Samar da Wutar Lantarki, Dokta Joy Ogaji, ta ce matsalar na da alaƙa da bashin da ya yi wa ɓangaren wutar lantarki ƙatutu.

Ta bayyana cewa gwamnati na bin kamfanonin da ke samar da wutar lantarki bashin kusan Naira tiriliyan 6.8, mafi yawansa yana da alaƙa da tashoshin wutar lantarki masu amfani da gas.

Ta ce: “An kafa kamfanin Kamfanin Sayen da Sayar da Wutar Lantarki na Najeriya domin ya riƙa sayen wuta daga kamfanonin samar da wuta sannan ya biya su gaba ɗaya.

“Amma tun daga 2013 har zuwa yanzu ba su taɓa biyan cikakken kuɗin da ake bin su ba, wanda hakan ya sa bashin ya kai kusan Naira tiriliyan 6.8.”

Ogaji ta ƙara da cewa kamfanonin da ke samar da gas yanzu sun fara ƙin bayar da gas sai an biya su kuɗinsu nan take, wanda hakan ka iya ƙara rage samar da wutar lantarkin da ake samu.

Ta ce: “Masu samar da gas sun faɗa mana cewa idan muna buƙatar gas dole mu biya kuɗin da ake bi tun da farko. Muna binsu kuɗi da yawa, kuma wannan na ɗaya daga cikin manyan dalilan da ya sa ake fama da rashin wuta a Najeriya.”

A sassa daban-daban na ƙasar, jama’a da ’yan kasuwa sun riga sun fara fuskantar koma baya sakamakon matsalar.

Kamfanonin rarraba wutar lantarki da dama sun fara raba wuta na ’yan sa’o’i, wato raba wutar lantarki ta yadda wasu yankuna za su riƙa samun wuta na ’yan sa’o’i ko ma su kwashe kwanaki ba tare da wuta ba.

A Jihar Legas, wasu mazauna jihar sun fito zanga-zanga saboda fama da rashin wuta da suke yi.

Wata mazauniya jihar, Misis Oyinlola, ta ce matsalar ta jefa iyalinta cikin damuwa.

Ta ce: “Yanzu kusan makonni uku kenan ba mu samu wuta mai kyau ba. Ba ma iya caja wayoyinmu, abincin da ke cikin firiji yana lalacewa, kuma yara suna shan wahala saboda zafi.”

Haka kuma ƙananan ’yan kasuwa suna fama da matsalar.

A Kano, wani sana’ar walda mai suna Musa Abdullahi, ya ce yanzu yana kashe dubbai a kullum wajen sayen fetur domin kunna janareta saboda rashin wutar lantarki.

Kamfanonin rarraba wutar lantarki sun nemi afuwar jama’a, inda suka ce matsalar ta samo asali ne daga ƙarancin gas da sauran ƙalubale da ke hana tashoshin wutar lantarki samar da isasshiyar wuta a faɗin ƙasar.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *