Sarki Sanusi Ya Goyi Bayan Karfafa Tattalin Arzikin Mata

[ad_1]

Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya ce; ya kamata a yi watsi da labaran da ke nuna yadda mata ke shiga harkokin tattalin arziki a matsayin wani ra’ayi na kasashen waje, yana mai jaddada cewa; Musulunci ya bai wa mata ‘yancin cin gashin kai.

Sanusi ya bayyana haka ne, a lokacin kaddamar da manufar karfafa tattalin arzikin mata (WEE) a hukumance ga Jihar Kano, wanda aka bunkasa ta hanyar hadin gwiwa da Cibiyar Bincike da Ayyuka (dRPC), tare da tallafin abokan hadin gwiwa da suka hada da Ford Foundation, Asusun Kalubalantar Kasuwancin Afirka da Gidauniyar Gates.

  • Kawar Da Dukkanin Haraji Kan Hajojin Da Ake Shigarwa Kasar Sin Daga Afirka Zai Bunkasa Cinikayyar Albarkatun Gona Na Afirka Ta Kudu
  • Kudaden Shiga Na Masana’Antun Kimiya Da Fasaha Na Kasar Sin Ya Karu Da 16.1% a Watannin Janairu Da Fabrairun Wannan Shekara

Sarkin ya ce, ci gaban al’ummar Musulmi na farko, ya ginu ne a kan yadda mata za su shiga harkar kasuwanci da bayar da tallafin karatu da kuma jagorancin al’umma, inda ya ce; karfafa wa tattalin arzikin mata, ya yi daidai da koyarwar Musulunci da kuma tarihin Kano.

A cewarsa, Kano ba za ta iya samun ci gaba mai dorewa ba, idan har mata suka ci gaba da zama saniyar ware.

“Tarihinmu da imaninmu a bayyane yake, domin kuwa, Musulunci ya bai wa mata ‘yancin mallakar kadarori, gado, kasuwanci da kuma harkokin tattalin arziki mai zaman kansa. Dole ne mu yi watsi da duk wani labari da ke nuna karfafa tattalin arzikin mata a matsayin bako ga kimarmu,” in ji shi.

Sanusi ya kara da cewa, idan har Kano za ta yi gogayya a fannin tattalin arzikin duniya, dole ne ta yi amfani da basirar mata da kuma samar da ayyukan yi, tare da tabbatar da cewa; ‘ya’ya mata sun samu ilimi da fasahar zamani da ake bukata a tattalin arzikin zamani.

Har ila yau, sarkin ya yi alkawarin tallafa wa Majalisar Masarautar Kano, wajen inganta manufofin, gami da bayar da shawarwari kan ilimin ’ya’ya mata, kula da zamantakewar al’umma da kuma karbuwar da al’umma ke yi na sana’ar mata.

Da yake yin jawabi a wajen taron, Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, wanda kwamishinan raya karkara da al’adu, Abdulkadir Abdulsalam ya wakilta, ya bayyana kaddamar da manufofin a matsayin wani ci gaba a yunkurin jihar, na samar da ci gaba.

Ya ce, gwamnati ta fara aiwatar da matakan tallafa wa mata ta hanyar kason kasafin kudi da kuma bayar da tallafin naira 50,000 ga mata 5,200 a duk wata a fadin kananan hukumomi 484 na jihar.

Ita ma wadda ta kafa kungiyar Isa Wali Empowerment Initiatibe, Maryam Uwais, ta bukaci masu ruwa da tsaki, da su tabbatar ba a bar matan karkara da ‘yan mata a baya ba.

Manufar shirin na nufin fitar da mata kimanin miliyan biyu daga kangin talauci tare da ba da gudummawar kusan kashi 30 cikin 100 na ci gaban tattalin arzikin Kano.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *