Rashin Nasara A Hannun Koriya Ta Kudu Ba Zai Sanyaya Ƙwazonmu Ba – Kociyar D’Tigress
[ad_1]
Kociyar babbar ƙungiyar ƙwallon kwando ta matan Nijeriya wadda ake kira D’Tigress, Rena Wakama, ta ce rashin nasarar da suka yi a hannun Koriya ta Kudu ba zai sanyaya ƙwazon tawagarta ba, tana mai cewa za su dawo kan turbar nasara.
Tawagar ta Nijeriya ta sha kashi da ci 77–60 a wasan da suka buga ranar Alhamis a gasar neman tikitin shiga FIBA Women’s Basketball World Cup. Wannan shi ne karo na farko da D’Tigress ta sha kashi a hannun Koriya ta Kudu, bayan an tashi 36–32 a rabin farko na wasan.

- Osimhen Ya Lashe Kyautar Gwarzon Dan Wasan Kwallon Kafa Na Bana A Kasar Turkiyya
- Nijeriya Ta Koma Matsayi Na 26 A Jadawalin Iya Taka Leda Na Hukumar FIFA
A wasan, Victoria Macaulay, wacce ta kasance ‘yar wasa mafi ƙwarewa (MVP) a wasan farko da suka buga da Colombia, ita ce ta fi taka rawa ga Nijeriya inda ta zura maki 22.
D’Tigress za ta fafata da Philippines a ranar Asabar a wasa na gaba, kafin ta kara da ƙasashen Turai da suka haɗa da Faransa da Jamus.

Wakama ta yaba da ƙoƙarin tawagar Koriya ta Kudu, tare da jaddada cewa za su yi amfani da darussan da suka koya daga wannan rashin nasara domin inganta bangarorin kai hari da kuma shiri mafi kyau a wasanni masu zuwa.
[ad_2]
Source link