Barazanar Trump: Ya kamata shugabannin Najeriya su farka daga bacci — Bishop Kukah




Bishop Matthew Kukah, na Cocin Katolika da ke Jihar Sakkwato, ya ce barazanar da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi na kawo wa Najeriya ya farkar da shugabannin ƙasar nan.

Trump, ya zargi Najeriya da cin zarafin Kiristoci tare da barazanar janye tallafin Amurka ko kuma ɗaukar matakin soja domin “ceto Kiristoci” a ƙasar.

Sai dai Shugaba Bola Tinubu, ya musanta wannan zargi, inda ya bayyana cewa Najeriya kasa ce mai cikakkiyar dimokuraɗiyya mai mutunta ’yancin yin addini.

Da yake jawabi a wajen bikin cika shekaru 60 na ɗan jarida Reuben Abati a Jihar Legas, Kukah, ya ce kalaman Trump na nuna akwai matsaloli a Najeriya.

“Muna ganin Trump a matsayin  matsala. Amma Trump alama ce ta rashin lafiyar da ke cikin ƙasarmu,” in ji Kukah.

“Ko Trump ne ko wani daban ya tunzuramu, lokaci ya yi da Najeriya za ta farka.”

Ya kuma soki rashin wuraren yawon buɗe ido da abubuwan tarihi da za su nuna ainihin abubuwan da Najeriya ta mallaka.

“Idan wani ya zo Najeriya yau, ina za ka kai shi? Dole mu sake gina ƙasarmu da kuma bayyana tarinhinmu a matsayin ’yan ƙasa,” in ji shi.

Kukah ya yi kira ga ’yan Najeriya da su yi tunani mai zurfi tare da ɗaukar nauyin gina ƙasa mai haɗin kai.




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *