Ghana Ta Sallami Kocinta Kafin Fara Gasar Kofin Duniya
[ad_1]
Hukumar ƙwallon ƙafa ta Ghana ta sallami kocin tawagar ƙasar, Otto Addo, bayan rashin nasara da suka yi a wasannin sada zumunta.
Ghana ta sha kashi da ci 2-1 a hannun Jamus a ranar Litinin, sannan Austria ta doke ta da ci 5-1 a ranar Juma’a.
- El-Rufai Ya Koma Kotu Bayan Rasuwar Mahaifiyarsa
- Babban Editan LEADERSHIP, Azu, Ya Samu Lambar Yabo Ta NUJ Kan Ƙwarewar Aikin Jarida
Wannan ya sa tawagar ta yi rashin nasara a wasanni huɗu a jere.
Tawagar Black Stars na cikin rukuni ɗaya da Ingila, Panama da Croatia a gasar kofin duniya.
Duk da suna da manyan ‘yan wasa kamar Antoine Semenyo da Mohammed Kudus, sun kasa zuwa gasar cin kofin Afirka ta 2025.
Bayan wasan Jamus, hukumar ƙwallon ƙafa ta ƙasar ta ce ta rabu da kocin nan take, kuma za ta sanar da sabon koci nan ba da jimawa ba.
Addo ya fara aikin horar da tawagar ne a watan Maris ɗin 2024.
Za a fara gasar kofin duniya a ƙasashen Canada, Mexico da Amurka daga ranar 11 ga watan Yuni zuwa 19 ga watan Yulin 2026.
Ghana za ta fara wasa da Panama a ranar 18 ga watan Yuni, sannan ta buga da Ingila a ranar 23, kafin ta kara da Croatia ranar 27 ga watan Yuni.
[ad_2]
Source link