Ministan Wajen Kasar Sin Ya Yi Kira Da A Kawo Karshen Matakan Soji A Gabas Ta Tsakiya

[ad_1]

Ministan ma’aikatar harkokin wajen kasar Wang Yi, ya yi kira ga dukkanin sassa masu ruwa da tsaki a rikicin da ya barke a yankin gabas ta tsakiya, da su gaggauta dakatar da matakan soji a yankin, kana su himmatu wajen dakile kara tabarbarewar yanayin da ake ciki.

Wang, ya yi kiran ne yayin tattaunawar da ya yi ta wayar tarho a jiya Alhamis, tare da takwaransa na Masar Badr Abdelatty, yana mai cewa tsawaitar tashin hankalin da ya barke zai haifar da karin illoli, da gurgunta tattalin arzikin yankin tare da illata tsaro. Ya ce Sin a shirye take ta yi aiki tare da Masar, da sauran kasashen yankin wajen tabbatar da zaman lafiya mai nagarta.

A nasa bangare kuwa Badr Abdelatty, cewa ya yi Masar ta damu matuka da barkewar rikicin, ya kuma jinjinawa matsayar kasar Sin ta adalci, da aniyarta ta ci gaba da tuntuba da nufin yayyafawa wutar rikicin ruwa.

A wani ci gaban kuma, Wang Yi ya zanta ta wayar tarho tare da takwaransa na Cuba Bruno Rodriguez, bisa bukatar hakan daga bangaren Cuba. Kuma sassan biyu sun amince da kara zurfafa gina dangantaka tsakanin sassan biyu. (Saminu Alhassan)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *