Matsalar Tsaro: Za a sake buɗe wasu makarantu a Neja

[ad_1]



Gwamnatin Jihar Neja ta sanar da cewa za ta sake buɗe makarantu ne a wasu ƙananan hukumomi huɗu kacal daga cikin ƙananan hukumomi 25 da ke faɗin jihar da aka rufe a dalilin matsalar tsaro.

Ƙananan hukumomin da aka amince za a buɗe makarantu a cikinsu sun haɗa da Bida, Suleja, Chanchaga, da kuma wasu sassan Bosso.

Kwamishiniyar Ilimi ta Firamare a Jihar Neja, Dokta Hadiza Asabe Mohammed, ce ta bayyana hakan a ranar Litinin yayin wani taron masu ruwa da tsaki gabanin buɗe makarantun.

Ta ce daga cikin makarantun kwana 45 da ke faɗin jihar, makarantu 18 kacal ne ke cikin ƙananan hukumomin Bida, Bosso, Suleja da Chanchaga waɗanda aka bai wa izini domin sake buɗewa.

Dokta Hadiza ta ce gwamnati ta amince makarantu za su riƙa buɗewa a matakai, gwargwadon yanayin tsaro da aka samu a sassa daban-daban na jihar.

Ta ce “za a fara buɗe wasu makarantu ne a ranar Litinin, 12 ga Janairu, 2026.

“Mun amince a cikin kwamitin da ke duba batun tsaro cewa ba za a buɗe dukkan makarantu lokaci guda ba, saboda yanayin rashin tsaron da muke ciki a Jihar Neja.

“Da farko, za mu buɗe makarantu a Chanchaga, da wasu sassan Bosso, da kuma yankin Suleja da Bida. Amma wannan buɗewar ta taƙaita ne ga makarantun da ke cikin birane da garuruwa kawai. Makarantun da ke wajen birane a waɗannan ƙananan hukumomi ba za a buɗe su ba a wannan lokaci.”

Kwamishiniyar ta ƙara da cewa, an umurci shugabannin ƙananan hukumomi da su ɗauki jami’an tsaron al’umma domin kula da tsaro da kare makarantu a yankunansu.

Ta kuma bayyana cewa gwamnati ta shirya tsarin koyarwa ta yanar gizo (online) domin tabbatar da cewa ɗalibai a dukkan sassan jihar ba su rasa damar samun ilimi ba, musamman a wuraren da ba a buɗe makarantu ba.

A nata jawabin, Darakta Janar ta Hukumar Ilimi da Gyaran Makarantu ta Jihar Neja, Hajiya Maimuna Mohammed, ta ce gwamnati ta haramta wa makarantu masu zaman kansu gudanar da makarantun kwana ga yara ‘yan aji na firamare da na yara ƙanana (nursery).

Ta ce wannan mataki na daga cikin ƙoƙarin da gwamnati ke yi na ƙara kare lafiyar yara da tabbatar da tsaro a makarantun jihar.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *